Wasu ’yan Bindiga da ake zargin ’yan daba ne, sun kai hari kasuwar Agbedo Akpanya da ke karamar hukumar Oduli ra jihar Kogi, inda suka kashe wani mai suna Johanson da kuma sace wasu da dama.
Bayan sace mutanen dai, ’yan bindigar sun kuma bukaci a ba su Naira miliyan 20 a matsayin kudin fansar wadanda suka sace din.
- Labarin kudurin sauya wa Kaduna suna zuwa Zazzau na kanzon kurege ne — Sanata
- Jamus za ta sanya wa masu amfani da iskar gas sabon haraji
Rahotanni dai na nuna cewa ’yan daban unguwa ne suka dirar wa kasuwar da misalin karfe 2:00 na rana a kan babura, inda suka fara harbi kan mai uwa da wabi.
A nan ne daya daga harsashinsu ya shiga har shagon marigayin ya kashe shi, yayin da suka yi awon gaba da abokinsa da suke tare mai suna Edwin da sauran mutane da dama da ke kasuwar zuwa daji.
Wasu daga cikin iyalan wadanda aka sace ne suka bayyanana wa Aminiya cewa ’yan bindigar sun bukaci a biya su kudin fasar.
Kakakin ’yan sandan jihar, William Aya, ya ce ba su kai ga gano inda ’yan daban suka kai wadanda suka sace ba, sai dai rundunar ta tura tawaga ta musamman yankin don yin farautarsu.
Kazalika, ya ce sun hada gwiwa da sauran masu ruwa da tsaki a yankin don ganin an shawo kan lamarin da kuma tabbatar da kanlmo wadanda suka aikata ta’asar.
Wannan dai shi ne karo na uku da ’yan bindiga suka kai hari kasuwar, inda suka sace mutane da kuma bukatar kudin fansa