✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa, sun kashe mutane da dama a ƙauyen Kano

A yanzu shi ne Karaye tana bukatar dakarun soji su kawo mana dauki saboda wadannan hare-hare.

Ana fargabar cewa wasu ’yan bindiga sun kwashe wani adadi da jama’ar kauyen Yola da ke Karamar Hukumar Karaye a Jihar Kano.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, lamarin na zuwa ne bayan wasu ’yan bindiga da ake zargin ’yan daban daji sun kai hare-hare a yankuna daban-daban na kauyen.

Bayanai sun ce hare-haren da aka kai yankuna daban-daban sun yi sanadiyyar mutuwar jama’a da dama yayin da aka yi garkuwa da wasu.

A cewar wani mazaunin kauyen da ya bukaci a sakaya sunansa, hare-haren sun auku a yankuna daban-daban na kauyen da ba zai iya fayyace adadin mutanen da aka kashe ko aka yi garkuwa da su ba.

“Na samu labarin cewa a rana ta farko sun sace mutum huud sannan sun kashe wasu mutum biyu.

“Haka kuma a rana ta biyu sun kashe karin wasu mutum biyu tare da garkuwa da mutum daya.

“Sai dai ba ni da tabbaci kan alkaluman mutanen da aka sace ko aka kashe.

“Amma ba na tantamar cewa an dauke wasu mutane kuma an kashe wasu.

“Abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne Karaye tana bukatar dakarun soji su kawo mana dauki saboda wadannan hare-hare,” a cewarsa.

Rahotanni sun bayyana cewa, a bayan nan yankunan Karamar Hukumar Karaye da Rogo na fuskantar matsalolin tsaro saboda kusancinsu da Jihohin Kaduna da Katsina.

Ana iya tuna cewa, a watan Afrilun da ya gabata ne wasu ’yan daban daji suka kashe wani mutum daya tare yin garkuwa da wani dan kasuwa a Kauyen Gangarbi da ke Karamar Hukumar Rogo, Alhaji Nasiru Na’ayya.

Kazalika, a shekarar 2021 ce Masarautar Karaye ta yi koken yadda ake samun kwararowar masu hakar ma’adanai daga Jihar Zamfara.

Wasu majiyoyi sun ce tuni masarautar ta dauki matakam da suka dace domin yi wa tufkar hanci.

Sai dai ƙoƙarin da wakilinmu ya yi domin jin ta bakin mai magana da yawun da rundunar ’yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ci tura a yayin da bai amsa kiran wayarsa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.