✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun yi garkuwa da matar Dagaci da danta a Kano

CP Dauda ya ce kawo yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike.

Wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da matar Dagacin Kauyen Nasarawa da ke Karamar Hukumar Tsanyawa a Jihar Kano.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Halima Kabiru mai shekaru 38 da danta Dahiru Kabiru mai shekaru 20 sun fada hannun ’yan ta’addan ne a ranar Lahadin da ta gabata.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kano, CP Mamman Dauda ne ya tabbatar da hakan a wata hira da ya yi da manema labarai a wannan Talata a birnin na Dabo.

CP Dauda ya ce kawo yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano masu garkuwa da mutanen tare da wadanda lamarin ya shafa.

“Bayan samun labarin, nan da nan muka kafa tawagar ceto a sassan da ke makwabtaka da su, wadanda ke aiki tukuru domin ceto wadanda abin ya shafa ba tare da sun ji rauni ba.”

Ya kuma kara da cewa, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an cafke wadanda ake zargin.