✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da Hakimi sun bukaci Naira miliyan 40

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun shiga unguwar Gayari da ke karamar Hukumar Gummi a jihar Zamfara, yau Juma’a sun yi garkuwa da…

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun shiga unguwar Gayari da ke karamar Hukumar Gummi a jihar Zamfara, yau Juma’a sun yi garkuwa da Hakimin garin da dansa, sannan sun bukaci jama’a su hada masu Naira miliyan 40.

Mazauna garin sun shaidawa wakilinmu cewa, ‘yan bindigar sun shiga garin ne sama da mutum 12 a babura, sannan suka shiga cikin fadar Basaraken garin, Alhaji Hassan Muhammad Gayari, tare da dansa.

Rahotan ya kara da cewa, ‘yan bindigar sun bukaci jama’ar garin da su hada Naira miliyan 40 don su dakatar da kai masu hari.

Kakakin hukumar ‘yan sandan jihar SP Muhammad Shehu, ya tabbatar da aukuwar harin kuma ya ce a yanzu haka suna ci gaba da bincike kan lamarin.