✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dan shekara 11 a Abaji

Wasu ‘yan bindiga da ake zarginsu masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani yaro dan shekara 11 mai suna Gbenga Segun, a…

Wasu ‘yan bindiga da ake zarginsu masu garkuwa da mutane ne sun yi garkuwa da wani yaro dan shekara 11 mai suna Gbenga Segun, a Unguwar Abatuwa da ke karamar hukumar Abaji babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin unguwar da ya nemi wakilinmu da ya sakaya sunansa ya ce, `yan bindigar sun yi garkuwa da yaron ne da misalin karfe 1:45 na daren ranar Asabar.

Ya ce, a lokacin da ‘yan bindigar suka shiga gidan su yaron sun yi harbi a sama sannan msuka balle kofar gidan suka yi awon gaba da yaron.