’Yan bindigu sun sako ragowar yara 12 da suka rage a hannunsu daga cikin yara 83 da suka sace a kauyen Wanzamai da ke Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.
A ranar Laraba ’yan bidaiga suka sako ragowar yaran bayan karbar kudin fansa Naira dubu 500, amma sun harbe daya daga cikin yaran har lahira.
- An yanke wa wanda ya lalata ’yar makwabcinsa daurin rai-da-rai
- An kwantar da magidanci a asibiti bayan matarsa ta yi masa duka
Kafin yanzu dai ’yan ta’addan sun sako 70 daga cikin yaran, amma wani mazaunin yankin mai suna Umar Hassan ya ce yanzu yara uku ke nan suka kashe.
A watan jiya ’yan bindiga suka yi awon gaba da wasu mutane, ciki har da mata a lokacin da suke tsaka da aiki a gonaki.
Kananan yaran kuma an yi awon gaba da su ne a lokacin da suka je neman icen girki a daji.
Akasarin wadanda ’yan ta’addan suka yi awon gaba da su sun fito ne daga kauyen Wanzamai.
Daga bisani sun amince su sako yaran a kan kudin fansa Naira miliyan shida, amma da aka ba su miliyan uku sai suka ki sakin su, suka nemi a kara musu da sabbin babura guda biyu.
Duk da haka, sun ci gaba da rike ragowar yaran da sai yanzu da suka su bayan sun karbi karin Naira dubu 500.
Wakilinmu a Zamfara ya nemi kakakin ’yan sandan jihar, CSP Muhammad Shehu, domin samun karin bayani amma samun jami’in ya fasakara.