✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun sace likitoci da majinyata a Neja

Sun yi awon gaba da duk ma'aikatan da ake aiki a asibitin a wannan lokaci.

Akalla mutum biyu sun mutu, sannan an yi garkuwa da wasu da dama ciki har da likitoci da jami’an jinya da kuma ‘yan uwan majinyata sa’ilin da ‘yan bindiga suka kai hari a Babban Asibitin Abdulsalami Abubakar da ke Gulu a Karamar Hukumar Lapai ta Jihar Neja.

Aminiya ta gano cewa wasu daga cikin jami’an asibitin da aka yi garkuwar da su ya shafi har da iyalansu da sauransu.

Bayanai sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ne don kwaso jami’an kiwon lafiyar da za su kula da ‘yan uwansu da aka yi wa rauni a daji.

Wata majiya daga asibitin ta shaida wa Aminiya cewa, baki dayan ma’aikatan da suke bakin aiki a wannan rana da lamarin ya auku da kuma wasu majinyatan da rashin lafiyarsu ba ta tsanata ba an yi awon gaba da su.

An ruwaito cewa ‘yan bindigar wanda yawansu bai gaza dari ba, sun kai harin ne cikin dare da misalin karfe biyu da rabi zuwa uku.

An ce harin ya yi sanadiyar tarwatsa mazauna kauyen inda suka tsere suka bar gidajensu domin neman mafaka a makwabta.

Ya zuwa hada wannan labari, ‘yan sandan jihar ba su ce komai a kan lamarin ba, sai dai mai Mai Magana da Yawun rundunar, DSP Wasiu Abiodun, ya ba da tabbacin zai yi karin haske bayan sun kammala tattara bayanai.

%d bloggers like this: