’Yan bindiga sun sace gwarzon gasar karatun Alƙur’ani, Abdulsalam Rabi’u Faskari, tare da mahaifinsa da ’yan uwansa a Jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata a kusa da Labin Bangori, yayin da suke dawowa Faskari bayan Abdulsalam ya samu lambar yabo wadda Gwamna Dikko Radda ya ba shi saboda nasarar da ya samu a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Jihar Kebbi.
- NAJERIYA A YAU: Ko Sulhu Da ’Yan Ta’adda Zai Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Arewa?
- Hanyoyi 6 da mutum zai kare kansa daga tsananin zafi
Wani jami’in gwamnati a Faskari, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da sace su.
“Malam Rabe da ’ya’yansa biyar, ciki har da Abdulsalam, wanda aka sace su a Bangori a kan titin Yankara. Har yanzu ba mu ji komai daga gare su ba.”
Abdulsalam, wanda ɗalibi ne a sashen likitanci na Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya, ya samu matsayi na farko a gasar a ɓangaren maza bayan ya haddace Alƙur’ani.
Har yanzu ’yan sanda a Katsina ba su fitar da wata sanarwa kan lamarin ba.