✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

’Yan bindiga sun kashe ’yan sanda hudu a Imo

Sun kubutar da wasu masu laifi biyu da ake tsare da su.

’Yan bindiga sun kashe jami’ai hudu yayin wani hari da suka kai Ofishin ’yan sanda na Agwam da ke Karamar Hukumar Oguta ta Jihar Imo.

Rundunar ’yan sandan ce tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an kai harin ne cikin daren Juma’a wanda ya yi sanadiyar mutuwar jami’anta hudu.

Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar, CSP Michael Abattam, ya ce maharan sun kona ofishin, sannan sun kubutar da wasu masu laifi biyu da ake tsare da su.

Jaridar Vanguard ta rawaito wata majiya na cewa, maharan sun yi harbe-harbe kana suka tayar da bam wanda ya yi sanadiyar konewar ofishin.

Da yake yi wa manema labarai karin haske kan harin a ranar Asabar, Abattam ya ce Kwamishin ’Yan Jihar, CP Mohammed Ahmed Barde, ya kai ziyarar gani da ido inda harin ya auku da kuma karfafa wa jami’ansu gwiwa.

“A ranar 05/8/2022 da misalin karfe 2300, ’yan ta’addan da ake zargin IPOB ne da ’yan bangan ESN, sun kai hari Ofishin ’Yan Sanda na Agwa.

“Maharan zun zo ne a cikin motoci guda biyu da wata tifa, inda suka yi harbe-harbe, sannan suka yi amfani da tifar wajen fasa kofar shiga ofishin, kana suka jefa abubuwa masu fashewa.

“Jami’an ’yan sandan yankin sun yi kokarin mayar da martani ga maharan inda aka yi musayar wuta, an halaka ’yan ta’addan da dama yayin da sauran suka tsere a motarsu,” inji Kakakin ‘yan sandan.

%d bloggers like this: