An yi jana’izar ‘yan bangar da ‘yan bindiga suka bude musu wuta a lokcin da suke kokarin kwato mutanen da ‘yan bangar suka yi garkuwa da su.
‘Yan bindigar sun yi garkuwa da mutum 30 bayan sun shafe awanni suna cin karensu babu babbaka a Karamar Hukumar Nasarawa ta jihar Nasarawa.
- Za a yi wa jaririyar da aka yi wa fyade tiyata
- Sojoji sun kwato mutumm 17 a hannun ‘yan bindiga
- ‘Yan bindiga: Sojoji sun bude sansani a Faskari
“Mun binne ‘yan banga guda biyu da ‘yan bidiga suka kashe a kan Dutsen Onda”, inji shugaban karamar hukuman, Muhammad Otto.
Mazauna sun ce maharan kimanin su 50 a kan babura sun tare hanyar Udege zuwa Loko na awanni inda suka kwashi mutanen a cikin daren Litinin.
Otto ya ce, “‘Yan bindigar sun kashe ‘yan banga guda biyu a kan Dutsen Onda, a kwaton baunar da suka yi wa ‘yan bangar da suka bi su domin kwato mutanen aka yi garkuwa da su”.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar ASP Nansel Ramhan bai amsa kiran wakilinmu ba domin karin bayani.