✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 8 sun raunata wadansu a yankin Giwa

A ranar Juma’ar da ta gabata ce da misalin karfe 11:30 na dare, wadansu ’yan bindiga masu garkuwa da mutane suka kewaye kauyen Sabon Sara da…

A ranar Juma’ar da ta gabata ce da misalin karfe 11:30 na dare, wadansu ’yan bindiga masu garkuwa da mutane suka kewaye kauyen Sabon Sara da ke Gundumar Kidandan a Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.

Aminiya ta ziyarci Asibitin Kauran Wali da ke Marabar Gaskiya, Kofar Kibo, Zariya, inda aka kawo wadanda suka samu raunin harbin bindiga su takwas, kuma daya daga cikinsu mai suna Salisu Usman wanda aka fi sani da Mati. ya ce, “A ranar Juma’a da misalin karfe 11:30 na dare, wadansu har sun kwanta sai wadansu da ba mu san ko su wane ne ba suka zu kauyenmu na Sabon Sara da ke yamma da Kidandan domin su sace wani mutumin kauyen namu mai suna Alhaji Nasidi su tafi da shi, sai ba su same shi ba, sai suka nemi daukar matarsa. Sai hayaniya ta fara tashi a kauyen mutane suka firfito domin su kawo dauki. Ganin haka sai ’yan bindigar suka fara harbin kan mai uwa da wabi, inda  suka harbi mutum 14  takaws daga cikinmu suka rasu, mu kuma aka kawo mu asibiti.”

Ya kara shaida da cewa, “Wadanda suka rasa rayukansu nan take mutane bakwai ne, akwai Ibrahim Bakanike da Lawal Sarkin Fawa da Lawal Bello da Tukur Bilyaminu Kafinta da Umaru Abdullahi Mairake. Akwai kuma wanda bindaga ta yi masa lahani sosai mai suna Muhammadu, sai kuma mace mai suna Fatima Ahmed, wacce ita ma ta rasu a sanadiyyar firgicewa da ta yi kuma dukansu an yi jana’izarsu. Mu kuma da aka kawo asibiti a sanadiyyar harabin bindiga mu takwas ne, da ni mai magana Salisu Usman Mati da Malam Abdullahi Umar da Aminu Ya’u da Rabilu Isa da Shu’aibu Ya’u da Muhammadu Musa da Ibrahim Sani da kuma Malam Sani Ahmed Buzu. Sai mutum na tara wanda aka kawo mu tare da shi, wanda shi ba harbin bindiga ba ne mai suna Yahuza Tukur. Shi saboda rudewa da firgici ne jininsa ya hau. To ka ji abin da ya faru da al’ummar kauyenmu ke nan.”

Da Aminiya ta tambayi Salisu Usman Mati cewa ba su da jami’an tsaro ne a garin? Sai ya ce, “Ba su a cikin garinmu amma akwai jami’an soja da aka aje a Kidandan saboda yawan kashe mutane da sacewa domin neman kudin fansa, wanda shi ne dama yake damunmu. A ’yan shekarun nan duk kewayen nan namu, sojoji sun kawo mana dauki a lokacin da abin ya faru sai dai ko kafin su zo, su maharan sun gudu.”

Ya kara da cewa dama wannan ba shi ne karo na farko ba, domin wata biyu da suka wuce sun kashe musu mutum biyar a gona. “Sai dai kwaso su muka yi aka kawo su gida, aka yi masu jana’iza kuma duk da ba mu san ko su wane ne ba amma mu muna zargin Fulani ne suka yi mana wannan aika-aika domin su ne dama suke satar shanu tare da satar mutane domin neman kudin fansa,” inji shi.

Aminiya ta ji ta bakin babban likita mai kula da Asibitin Kauran Wali kan yadda aka kawo su, wato Dokta Abdulmumini Adamu Ibrahim ya ce: “Sojoji ne da ’yan uwansu suka kawo su da misalin karfe hudu na asuba, su tara kuma takwas daga cikinsu harbin bindiga ne, daya kuma hawan jini ne mai tsanani ya kamu da shi kuma mun ba su kulawa sosai, sai dai akwai daya da harbin ya karya masa hannu. Shi sun koma da shi gida domin su yi masa daurin gida kuma akwai wadanda muke sa ran cewa za mu sallame su nan ba da dadewa ba.”

Da yake bayani a lokacin da Aminiya ta tuntubi Sakataren Karamar Hukuma Giwa, Usman Isma’il ta wayar hannu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce a lokacin suna tare da Shugaban Karamar Hukumar Giwa, Injiniya Abubakar Shehu Lawal Giwa da kuma jami’an tsaro a makabarta wajen jana’izar wadanda suka rasu kuma bayan nan za su ziyarci asibiti domin duba wadanda suka samu raunuka. Ya ce jama’ar Sabon Sara su kwantar da hakalinsu, in Allah Ya yarda za su hada gwiwa da jami’an tsaro domin daukar mataki.

Da yake karin bayani, Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu A. Sabo ya ce mutanen gari sun samu nasarar kashe daya daga cikin maharan kuma daya da ke kwance a asibitin ya rasu.