✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan bindiga sun kashe mutum 11 a kauyen Filato

Wasu ’yan bindiga sun bude wuta kan mazauna kauyen Rim da ke cikin karamar hukumar Riyom da ke jihar Filato a cikin daren ranar Talata…

Wasu ’yan bindiga sun bude wuta kan mazauna kauyen Rim da ke cikin karamar hukumar Riyom da ke jihar Filato a cikin daren ranar Talata inda suka kashe mutum 11 suka yi wa da yawa rauni.
Wadanda lamarin ya rutsa da su ’yan kasuwa ne da suke dawowa daga cin kasuwar mako-mako a kauyen Makera a lokacin da ’yan bindigar suka bude musu wuta sanye da kayan sojoji.
Mai Magana da Yawun Rundunar ’Yan Sandan jihar Filato, Terna Tyopev wanda ya tabbatar da lamarin ya gargadi jama’ar yankin kada su dauki doka a hannunsu ta ramuwar gayya tun da ba a gano wadanda suka aikata lamarin ba.