✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan bindiga sun kai hari masallaci tare da yanka wani a Borno

Wasu ‘yanbindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram da muggan makamai sun afkawa wani masallaci a daren jiya a unguwar Sajeri, da ke wajen…

Wasu ‘yanbindiga da ake zaton ‘yan kungiyar Boko Haram da muggan makamai sun afkawa wani masallaci a daren jiya a unguwar Sajeri, da ke wajen birnin Maiduguri, inda suka yi wa wani mutum guda yankan rago a cikin  masallacin.

Ganau sun ce ‘yan Boko Haram din sun dirar wa unguwar ne a daidai lokacin da ake sallar Tahajjudi, suna harbe-harben kan mai tsautsayi, kafin daga bisani suka mai da hankali akan masallatan.

Babu dai karin bayani akan farmakin, sai dai wasu majiyoyin sun tabbatar mana cewar, harin da Boko Haram suka kai a masallacin ya haifar da rudani tare da turmutsutsi ga masallatan, inda kowa ya ranta a na kare domin ceton rai.