✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

”Yan bindiga sun kai hari gidan Magu

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, inda suka kashe dan sanda guda daya. Rahotanni na nuna cewa dai ‘yan…

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari gidan shugaban Hukumar EFCC, Ibrahim Magu, inda suka kashe dan sanda guda daya.

Rahotanni na nuna cewa dai ‘yan bindigan sun kai harin ne da misalin karfe 10 na daren jiya a gidan gonarsa da ke Karshi a Babban Birnin Tarayya Abuja, inda suka yi musayan harbi da ‘yan sandan da ke sintiri a gidan, har suka harbi dan sanda daya, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa nan take. Kuma wannan ne karo na biyu da aka kai irin wannan harin a gidan shugaban na EFCC.