✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan barandar kujerun aikin Hajji ba masu tsoron Allah ba ne – Salisu Musa

Alhaji Salisu Musa shi ne Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Filato, a tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana damuwarsa kan yadda ’yan barandar kujerun aikin…

Alhaji Salisu Musa shi ne Babban Sakataren Hukumar Alhazai ta Jihar Filato, a tattaunawarsa da wakilinmu ya bayyana damuwarsa kan yadda ’yan barandar kujerun aikin Hajji, ke kawo matsala ga maniyyata aikin Hajji: Haka ya yi bayani kan shirye shiryen hukumarsa da batun adashin gata da na muharramai da sauransu:

Aminiya: Wane kokari kuke yi don ganin kun magance matsalar ’yan baranda da suke karbar kudaden maniyata da sunan za su sayar masu da kujerun aikin Hajji a wannan hukuma?
Salisu Musa. Bisa gaskiya, ayyukan ’yan baranda a hukumar alhazai ta Jihar Filato, duk yadda mutum ya yi sai dai ya bar su da Allah. Saboda ni a wajena ’yan barandar nan ba masu tsoron Allah ba ne. Idan
mutum mai tsaron Allah ne ba zai cuci maniyyaci ba, a bar maniyyaci ya zo ya same mu ya biya kudin kujerarsa da kansa. Amma irin wadannan ’yan baranda sai su je su tsaya a kofar shiga wannan hukuma kamar masu gadi, suna jiran maniyyata su shigo. Bisa gaskiya da za su ji shawara ya kamata su yi tunani cewa aikin Hajji aiki ne na ibada, don haka idan suka kara wa maniyyaci kudi ba zai kare su da komai ba. Idan maniyyaci ya zo bai samu kujera ba su kyale shi. Za ka samu suna kara wa maniyyata kudin kujera kamar dubu 50 zuwa dubu 100. Wannan abin yana faruwa tun kafin na zo wannan hukuma, mun dauki matakai da dama na dakatar da wannan muguwar dabi’a amma abin ya gagara. Don haka mun bar su da Allah musamman ganin cewa wannan aiki ne na ibada.
Aminiya: Zuwa yanzu wadanne shirye-shirye kuka yi kan aikin Hajjin bana?
Salisu Musa: Bayan kammala aikin Hajjin bara, dama abu ne da aka saba, Hukumar Hajji ta kasa takan kira jihohi domin a zauna a duba irin nasarorin da aka samu a baya da kuma shirye-shiryen da za a yi kan aikin Hajji na gaba, domin a kara samun nasara a aikin Hajji mai zuwa.
Don haka, tuni mun riga mun yi wannan taro kuma an gudanar da wannan taro ne a karkashin Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar. A wannan taro kowa ya kawo shawarwari kan irin yadda za a samiu nasara a aikin Haji mai zuwa. A cikin shirye shiryen da aka fitar mana akwai maganar masaukan alhazai. Don haka a wannan mako da muka shiga duk sakatarorin alhazai na jihohin kasar nan, za mu tafi Saudiyya domin mu duba masaukan alhazanmu. Mu daidaita da masu ba mu hayar masaukan  Wannan shi ne muka fara yi a maganar shirye-shiryen aikin Hajjin bana.
Aminiya: Yaya maganar kudin adashin gata da kuke karba daga maniyyata a bana?
Salisu Musa: Wato shi adashin gata da muke yi wa maniyyata a nan jihar, ba a fara shi, sai an ji yawan kujerun da aka ba jihar. Zuwa yanzu an riga an raba wa jihohin yawan kujerun aikin Hajji mai zuwa.
Kuma a bana  an ba mu kujera 1,274  a bara an ba mu kujera 1300, wato an rage kujera 26 ke nan a bana kuma ba Jihar Filato ce kadai aka rage wa alhazai ba, an rage wa duk jihohin kasar nan yawan kujerunsu. kasar Saudiyya tana rage yawan alhazan ne saboda aikin da ake yi a Harami. Mun raba kujerun da aka ba mu, mun ajiye kujerun da za mu sayar ga alhazanmu, kuma mun ajiye kujerun da gwamnatin jiha
da kananan hukumomin jihar nan za su biya. Kuma an amince mana mu ci gaba da karbar kudin adashin gata na kamar kudin kujerar da aka biya a bara wato Naira dubu 600.  Don haka mun fara karbar kudin adashin gata kuma mun kusa kammalawa.
Aminiya: A shekarun baya, akwai alhazan da aka bari a nan jihar wadanda ba su samu tafiya aikin Hajji ba. Wane mataki kuke dauka don ganin alhazan sun samu tafiya a bana?
Salisu Musa: Mun yi tanadi mai karfi don ganin wadannan maniyyata sun samu tafiya aikin hajji a bana. In Allah Ya yarda wanda duk sunansa ke cikin wadancan maniyyata zai samu tafiya aikin Hajji a bana. Zuwa yanzu mun biya mutum 68 kudadensu da suka ce a biya su. Kuma yanzu akwai mutum 50 da suka rage su ne in Allah Ya yarda za su tafi aikin Hajji a bana.
Aminiya: Yaya maganar muharrami a bana?
Salisu Musa: Maganar muharrami ta zama dole ga duk mace maniyyaciya aikin Hajji. Domin dama a Najeriya ne ake yin sakaci da maganar muharrami, inda za ka ga ko’ina ana barin mata suna tafiya aikin Hajji ba tare da muharrami ba. Amma in ka dubi sauran kasashe za ka ga kowace mace tana tafiya da muharraminta. Don haka bullo da wannan shiri da aka yi ya taimaka kwarai da gaske wajen rage bata suna da wasu matan Najeriya suke yi a lokacin aikin Hajji.
Aminiya: Wane tallafi gwamnatin Filato take yi wa maniyyatan jihar?
Salisu Musa. A duk shekara gwamnatin Jihar Filato tana tallafa wa alhazan jihar nan, wajen sama musu masaukai masu kyau da inganci kuma a kusa da harami.  Bayan haka kan maganar kiwon lafiya gwamnatin jihar tana daukar nauyin likitoci da masu aikin jinya don kula da lafiyar alhazai tun daga nan gida har zuwa kasa Mai tsarki.
Aminiya: Mene ne sakonka ga maniyyata?
Salisu Musa. Sakona ga maniyyata shi ne duk maniyyacin da Allah Ya ba shi damar biyan kudin aikin Hajji ya yi kokari ya koyi yadda ake aikin. Domin idan mutum ya tafi aikin Hajji ba tare da ya san aikin ba, zai tafi yawo ne kawai. A wannan hukuma muna da malaman da suke tantance maniyyata idan suka samu ba ka san yadda za ka yi aikin Hajjin ba, za mu soke sunanka. Ko a bara mun samu irin wadannan maniyyata da muka hana su zuwa aikin hajji saboda ba su san yadda ake aikin Hajjin ba. A bana idan suka zo suka bayyana yadda ake aikin za mu bar su su tafi. Idan ba su sani za mu sake ajiye su sai badi, muna yin haka ne domin aikin hajji aikin ne na ibada.