✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Arewa mu gyara kura-kurenmu

Yan Arewa  mu gyara kura-kurenmu, musamman ganin kakar siya ta kunno kai. Dalilin wannan sakon nawa shine domin inyi tambihi ga mutanenmu na Arewacin Najeriya…

Yan Arewa  mu gyara kura-kurenmu, musamman ganin kakar siya ta kunno kai. Dalilin wannan sakon nawa shine domin inyi tambihi ga mutanenmu na Arewacin Najeriya domin mu yi karatun ta natsu domin mu. Da farin fari me yasa muke tayin kuskure ba ma ci gaba, kuma ba ma chanzawa. Annabi Muhammadu (saw) ya ce ba a cizon Mumini a rami daya. Da mu da manyanmu mun shiga rudu sosai. Bugu da kari mun rarraba kwarai da gaske. Kodayake akwai lokacin da mu hadewa, amma sai in lokaci ya kure muke hadewa.
A ra’ayina, siyasa abin yi ne, kuma ya kamata maza da matanmu da duk yaran da suka kai shekarun jefa kuri’a da mu tsunduma sosai wajen siyasa, domin mu ceto Arewa daga ‘yan bana bakwai, wadanda suke da manufar korarmu da muzantamu. Ba ma Arewa kadai ba har ma ilahirin kasar Najeriya na bukatar aikinmu na cetonta. Da fatan Allah maigirma ya shige mana gaba amin. Babban abin da ya kamata mu yi a wannan bangaren shi ne hada kai ba hada baki ba, kamar yadda Alhaji Abubakar Ladan ke fada. Hadin kanmu ya hada dukkanmu a siyasance, addinance da ilimance.
Dangane da hada kai a siyasance ya kamata mu zama tsintsiya madaurinki daya. A samemu a PDP a APC da duk wata jam’iyya mai rai, don mu auna mu lissafa, kuma mu nazarta mu ga yadda za mu kwace ragamar mulki. Ya kamata mu dauka kuma mu tabbatar da cewa PDP tamu ce, APC ma ta muce duk da bambancin manufa da abubuwan da suke yi. Dalilina kuwa shi ne a zabukan da suka gabata kamar na 2011, misali wadansunmu sun nuna tsohuwar jam’iyar CPC ta mai sallah ce kawai. Kuma PDP ta arna ce kadai. Gaskiya haka ba lissafi, kuma ba hikima cikin abin, hasalima ba gaskiya ba ne. Kuma ya haifar da matsala sosai. Allah ya kiyaye. Ya kamata mu gyara, kuma ya kamata mu rika wayarma da juna kai. Lokaci ya yi da za mu rika kwabar duk wani dan siyasa da zai yi amfani da addini ta hanyar da bai kamata ba.
A kwai addini a siyasa, kuma akwai bambancin addini, to amma ba a ce a yi amfani da damar ba a cuci wani ko wata ba.Ya kamata mu yi amfani da addini mu gina kasa, bisa karantawar Annabi Isa (as) da Annabi Muhammad (saw).Hausawa kan ce inda baki ya karkata nan yawu ke zuba, domin yadda siyasar Najeriya ke gudana kuma lokaci ya karato, ya kamata duk sa’ar da kugen siyasa ya motsa aka fito mana da nagartantun ‘yan siyasa a matakai daban – daban tun daga na Kansila har zuwa Shugaban kasa to mu hade mu zabi nagari, kuma koda daga wace jam’iyya ya fito.
Yanzu lokaci ne na zaben dan takara ba jam’iya ba.Kodayake wasu jam’iyyun kan tursasa wa dan takararsu in ya yi nasara day a yi abin da bai kamata ba. A nan sai mu kara hangawa mu ga wane ne zai tafi tare da mu cikin ikon Allah duk inda muka yi zai kasance tare da mu. Insha Allahu muna da kwakwalwa ta bambancewa da hangen nesa. Allah ya yi mana jagora amin.
Na biyu, aikin noma da kiwo lokaci ya yi da shugabannimu za su jajirce, domin ganin cewa an canza tsarin nomanmu da kiwo a ilahirin Arewa. Lokaci ya yi da shugabanninmu wadanda suka hada ‘yan majalisar zartarwa na tarayya, Gwamnoninmu na Arewa  da ‘yan majalisarsu  ta zartarwa da ‘yan majalisun tarayya da na Jihohi da Shugabannin kananan hukumomi da ‘yan majalisarsu da duk wani shugaba a kasa ko sama da a yi tsarin da zai farfado da noma da kiwo sosai, domin inganta masana’antu, samar da aikinyi, da gina Arewa ta yadda za ta rika samun kudin shiga ta tsayu da kafarta sosai.
Kusan dukiyar man fetur da ake sanmana ta kawo mana kaskanci da kashe mana zuciya. A gaskiya maganar takin zamani da  tantan da galmar shanu da ta hannu da sauran kayan aikin noma. Don haka ya kamata a yi tsari da zai sa su wadatu sosai, kuma cikin sauki. An ce akwai tallafi a man fetur aka cire aka tara kudin daban, har ga shi an haifi Sure-P don agaza wa masu neman aiki. Mene ne zai hana itama SURE-P bangaren Arewa ta fuskanci aikin noma da dangoginsa, domin ya habaka.
Sanin kowana akwai kasashe da yawa da ba su damai kuma suna da karfin tattalin arziki, wanda sukan jingina da noma. Ya kamata shuwagabanninmu su sani Allah zai tambayesu wannan aiki da yabasu, wannan amana da ya ba su. Suna ta kukan ba su da kudin shiga za su iya kafa gonaki manya-manya masu samar da kudin shiga . Gonar alkama da masara da lemu da ayaba da tumatir da kiwon dabbobi da sauransu.  Abin da ake so shi ne mayar da hankali da sa ido sosai. Lallai yadda Allah ya fitar da arziki ta fetur haka yake fitar da shi ga noma da kiwo. Wai shin akwai abin da ya fi noma da kiwo. Ni dai na sani ko fetur ko gas ko ma wani abu mai dangantaka da fetur aka sayar za a yi amfani da kudin a ci abinci ko sutura ku a sayi kujera da sauran kayan da ake samu ta silar gona.
[email protected] Mohammed Sani Garba