Shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles Yakubu Aiyegbeni ya samu nasarar sanya wa kulob din Readings na Ingila hannu a ranar da aka rufe kasuwar saye da sayar da ’yan kwallo a Nahiyar Turai.
Rahoton da kafar sadarwar wasanni ta Supersports.com ta kalato ya nuna dan kwallon mai kimanin shekara 32 tuni ya samu nasarar gwajin lafiyarsa (medical check up) da hakan ta sa ya rattaba wa kulob din hannu.
Yakubu dai ya koma kulob din Al-Rayyan da ke katar ne a shekarar 2012 bayan ya rabu da kulob din Blackburn Robers na Ingila.
dan kwallon ya samu nasarar zura kwallaye 114 a tsawon shekaru tara da ya kwashe a Ingila inda ya yi wasa a kulob din Postsmouth da Middlesbrough da na Eberton da Leicester City da kuma Blackburn Robers.
Yakubu ya yi wa kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles  wasanni sau 57 kuma ya samun nasarar zura kwallaye 21.
Yakubu Aiyegbeni ya koma kulob din Readings
Shahararren dan kwallon Najeriya Super Eagles Yakubu Aiyegbeni ya samu nasarar sanya wa kulob din Readings na Ingila hannu a ranar da aka rufe kasuwar…