✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yaki da rashawa nauyi ne kan ’yan Najeriya ba Shugaba Buhari kadai ba’

Alhaji Aminu Ibrahim No Delay sabon Shugaban karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa ne, a tattaunawarsa da Aminiya jim kadan da bayyana shi a matsayin wanda…

Alhaji Aminu Ibrahim No Delay sabon Shugaban karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa ne, a tattaunawarsa da Aminiya jim kadan da bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban karamar hukumar da aka gudanar a makon shekaranjiya, ya ce samun nasarar Shugaba Buhari ta yaki da cin hanci da rashawa za ta dogara ne kan sadaukarwar ’yan Najeriya. Kuma ya tabo batun ba kananan hukumomi ’yancinsu:

Aminiya: Me ya sanya kake son sake jagorantar karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa?
Alhaji Aminu: Kamar yadda ka ce in sake, to ba sakewa ba ce don ban rike karamar hukumar ta hanyar zabe ba. Gwamnatin Jihar Sakkwato ta wancan lokaci ta dauko ni ne saboda ina tsohon ma’aikacin karamar hukuma ta ba ni rikon kwarya, domin na yi shekara 35 ina aiki a kananan hukumomi daban-daban. Daga baya sai na ga ya dace in zo in yi wa ’yan uwana hidima da taimako a karkashin wannan gwamnati da ke da manufa irin tawa waton inganta rayuwar al’umma shi ne muka sanya gaba daga sama har kasa. Lokaci ya wuce da zan yi tunanin yin mulki don samun wani abu ina son bayan ba ni nan a gaya wa ’ya’yana mahaifinku ya yi aikin madalla, abu kaza da kaza da jama’a ke amfana da shi da sa hannuna ya Kasance, bukatata da wannan kujera taimakon jama’a da inganta rayuwa da yanayinsu.
Aminya: Gwamna Aminu Tambuwal ya goyi bayan dokar bai wa kananan hukumomi cin gashin kai, in dokar ta kasance mene ne alfanunta ga kasa musamman mutanen karkara?
Alhaji Aminu: Wannan dokar za ta yi amfani kwarai don kullum aka tashi sai ka ga an samu ci gaba don ana kara fahimtar yadda za a yi mulkin dimokuradiyya ga wanda ke mulki da wanda za a mulka a karamar hukuma domin ta talakawa ce. Amma yaya abu zai zama naka ba a ba ka ba, matukar babu ’yancin zama da kananan hukumomi don su san kudinsu da yadda ake kashe su wannan shi ne zai sa al’umma su mutunta abubuwan da aka samar masu don sun san da shawararsu da dukiyarsu ne aka yi wannan lamari. Za ka ga ci gaba ya samu irin wanda wannan jam’iyya ke nufi ba na tara dukiya ba, tunda jama’a ake nufi in an ba da dama aka yi gyaran wannan doka ta ba kananan hukumomi cin gashin kai to babu shakka za a samu ci gaba cikin kankanen lokaci musamman a karkara.
Aminiya: Gwamna da Majalisar Dokoki ta Jihar Sakkwato suna kokarin yin gyaran fuska ga dokar kananan hukumomi inda ake son rage wa’adin mulkin ciyamomi zuwa shekara biyu. Yaya kake ganin hakan ganin wadanda suka gaba ce ku sun koka da karancin wa’adin shekara uku ga samar da ci gaban al’umma mai nagarta?
Alhaji Aminu: To bisa gaskiya ban san dalilin da ya sanya aka yi tunanin rage tsawon shekarun shugabancin kananan hukumomin ba, amma abin da nake kallo in ka dubi rashin samun issashen lokacin aiki ne ke sanya mutum neman wa’adin mulki na biyu. Da mutum zai samu lokaci isasshe na aiki ba zai yi kokarin dawowa ba, don al’umma da kansa sun cimma kudirinsa na mulki. Gaskiya shekara biyu sun yi kadan kwarai ga mai mulki da har zai yi wani abin a-zo-a-gani zai fara dai don muna da matsalar gudanar da abubuwa in magajin mutum ya zo ba ya son karasawa, don an san ba shi ne ya tsara su ba komai amfaninsu ga rayuwar jama’a to ka ga yana da kyau a bai wa mai mulki isasshen lokacin da zai gane yana iya yin abu ko bai iyawa. Saboda haka shekara biyu me za su yi ga shugabancin karamar hukuma in aka dubi yadda ci gabanmu yake.
Mutanenmu na tsananin bukatar hanya da ruwa da ingatacciyar kiwon lafiya da inganta rayuwar matasa a fito da abubuwan dogaro ba sai aikin ofis ba. Ya kamata a sani dimokuradiyyarmu jaririya ce ci gabanmu karami ne ban san dalilin yin wannan doka ba duk da yana yiwuwa akwai hujjojin da suka fi nawa. Amma a tunanina shekara biyu sun yi kadan mutum ya yi aikin da yake bukatar yi, yanzu ma shekara ta yi nisa babu kasafi tun da ba mu nan yaushe har ka yi kasafi ka fara abubuwan da ake bukata balle ka gama.
Aminiya: Shugaban kasa ya sanya yaki da rashawa a gaba, ka gamsu da tafiyar?
Alhaji Aminu: Nasarar Shugaba Buhari kan yaki da rashawa na kan wuyan ’yan Najeriya ne. Kowane abu yana samun nasara ne ta yadda mutane suka ba shi goyon baya, in al’umma na kyamar abu dole ne mutum ya bar shi. Misali a jihar nan tamu da al’umma suna nuna kyamar Area Boys da ba za su yi ba, amma da ba a kyamar su ga sunan muna tare da su. Misali za ka ga mutum ya debo kudin jama’a ya zo da su niki-niki amma mutane ba su kyamar su balle a ce ina ya samo wannan dukiya ba ruwan mutane da wannan su dai kawai a ba su, mutanen gidanku ba su kyamar abin da kake yi. Da akwai akidar gudun wanda ya sato kudin gwamnati da dole mutum ya bari ba tare da zabi ba. Gaskiya akwai bukatar a fadakar da jama’a su ba da goyon baya a gina kasa da jama’a nagari, domin sata kamar iska ce in ta gurbace duk wanda ya shake ta za ta yi masa lahani. Don haka kowa ya zo a taimaki Shugaba Buhari a tsalkakar da kasar nan, a ba da goyon baya kowa ya zama kamar Sardauna a rika tunawa da shi kan taimakon kasa da jama’a. Ba don Shugaba Buhari muka samu ba da kasar nan babu ita, sai dai suna kawai komai ya tarwatse ana kisan mutane ko’ina, tunda an samu kwanciyar hankali an daina kisan mutane, a taimaki kasar nan, wannnan yaki da Buhari ke yi, musamman dawo da martabar noma da yake kokari don mu daina dogaro da mai zalla saboda tattalin arzikinmu ya tsaya da kafafunsa mu yi kafada-da kafada da takwarorinmu na duniya.