✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yajin Aikin Jami’o’i: Gwamnati na neman raba kan malamai —NAAT

Kungiyar Malaman Fasaha ta Kasa (NAAT) ta ce akwai lauje cikin nadi a rahoton Kwamitin Nimi Briggs kan abin da ya shafi yarjejeniyar karin albashin…

Kungiyar Malaman Fasaha ta Kasa (NAAT) ta ce akwai lauje cikin nadi a rahoton Kwamitin Nimi Briggs kan abin da ya shafi yarjejeniyar karin albashin kungiyoyin jami’o’in.

Kungiyar ta ce kin sanya yarjejeniyar daidaita albashin da kwamitin ya yi a rahoton nasa, ba abin da zai haifar sai tsawaita yajin aikin kungiyoyin.

Shugaban kungiyar ta NAAT, Ineji Nwokoma ya zargi kwamitin da neman raba kan kungiyoyin ta hanyar bambamta tsarin albashinsu, sabanin abin suka cimma a tattaunawarsu.

Ya ce ko da sauran kungiyoyin jami’o’in sun janye nasu yajin aikin, to dakunan gwaje-gwaje da na lafiya, da gonakin makarantun za su kasance a rufe, matukar ba a gyara wannan matsala ba.

“NAAT za ta yi iya kokarinta wajen kin amincewa da bambamta albashin kungiyoyin duka, domin hakan zai haifar da wata matsalar ne bayan bai magance wata ba”.

“Don haka muna kira ga Kwamitin Nimi Briggs da ya dawo kan yarjeniyoyin da muka yi a zamanmu da su, saboda alamu na nuna ba shi da niyyar daukar wani mataki a madadin Gwamnatin Tarayya”, in ji shi.

Nwokoma ya kuma ce matakin gwamnatin na kin biyan albashin ma’aikatan saboda suna yajin aiki ya saba wa dokar Najeriya.