Yajin aikin da Kungiyar Masu Hada Burodi (AMBC) ta shiga a Jihar Kwara ya haifar da karancin burodi a fadin jihar.
Aminiya ta gano kungiyar ta tsunduma yajin aikin ne a karshen mako, domin nuna fushinsu a kan karancin fulawar da gidajen burido ke sarrafawa a jihar.
- An yi garkuwa da dan Majalisar Dattawa
- Zan tabbatar an yi wa masu yi wa kasa hidima a Katsina rigakafin COVID-19 – Masari
Masu gidajen burodin sun kuma yi kira ga gwamnati da masu ruwa da tsaki da su sanya baki domin kamfanonin fulawa su rika samar da ishasshiyar fulawa a jihar.
Mutane da dama a jihar, musamman wadanda ke yawan amfani da burodi sun shiga tasku a sakamakon haka, inda dole ta sa suke neman wata mafita.
Wata mai shago a kusa da kasuwar Mandate a Ilorin, Ummu Sa’ad, ta shaida wa wakilinmu cewa a baya masu gidajen burodi sun koka kan yadda farashin fulawa ya yi ta tashi, kafin daga baya su shiga yajin aikin.
Ta kara da cewa matakin nasu na iya haifar da karin farashin burodi a jihar.
Da yake tabbatar da shigarsu yajin aiki, Shugaban AMBC reshen Jihar Kwara, Abdulfatahi Alaba, ya ce tsadar fulawa da sukari ta shafi farashin burodi da dangoginsa.
Ya kara da cewa ko yaushe kamfanonin fulawa kan yi musu karin farashi sannan ga shi suna fama da karancin fulawar da za su rika amfani da ita wajen hada burodin.
“Ya kamata mutanen Kwara su fahimce mu, su ba mu hadin kai kan wannan al’amari, ba mu da nufin kawo tsanani ga abokan huldarmu.
“An kasa biyan bukatanmu, masu sana’ar burodi da dama a Kwara sun rufe wurarensu,” inji Alaba.