Yajin aiki da Kungiyar Kwadago (NLC) ta fara kan mafi karancin albashi ya hana kotu sauraron Shari’ar Rikicin Masarautar Kano.
A ranar Litinin da kungiyar ta fara yajin aiki ne ya kamata a fara sauraron shari’ar Dambarwar Sarautar Kano tsakanin Sarki Aminu Ado Bayero da Sarki Muhammadu Sanusi II.
Wakilinmu da ke Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Kano ya ruwaito cewa Mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman ya zo domin zaman, amma duk da haka jami’an NLC sun kulle harabar sun hana shiga.
Daga bisani wani jami’in kotun da ya nemi a boye sunansa ya sanar cewa an dage zaman saboda yajin aikin, ya kuma musanta yiwuwar gudanar da zaman kotun ta intanet ta kafar Zoom.
- NLC ta kashe wuta daga babbar cibiyar lantarkin Najeriya
- Yajin aiki: Maniyyatan Najeriya na cikin rashin tabbas
Sai dai kuma bai bayyana ranar da za ta saurari karar a nan gaba ba.
Haka dai na zuwa ne a daidai lokacin da yajin aikin NLC ya tsayar da harkokin aikin gwamnati da na kasuwanci da sauransu a Kano da ma fadin Najeriya.
Da farko wasu rahotanni na ikirarin cewa akwai yiwuwar kotun da ke Sakatariyar Audu Bako ta fara sauraron shari’ar ta intanet ta kafar Zoom.
Amma kotun ta ce babu zaman da za ta yi kai tsaye ko ta intanet.
Kwanaki 10 ke nan da ake kai ruwa rana a Kano bayan majalisar dokokin jihar ta yi gyaran fuska ga dokar masarautun jihar.
A ranar Alhamis din Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sa hannu kan sabuwar dokar da ta soke duk sabbin masarautun jihar guda biyar da tsohuwar gwamnatin Abdullahi Ganduje ta kirkiro.
Bayan nan ne aka naɗa Sarki Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano bayan tube Sarki Aminu Ado Bayero.
Wannan lamari dai ya kai kai ga gaban kuliya, inda Babbar Kotun Tarayya ta hana nada Sarki Sanusi II.
Daga bisani Babbar Kotun Jihar ta hana Sarki Aminu ayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, wanda bayan nan Gwamna Abba ya ba da umarnin a kama shi.
Bayan haka ne Babbar Kotun Tarayya ta ba da umarnin kama Sarki Sanusi II.
Ana iya tuna cewa a makon jiya Shugaban Alkalan Najeriya ya gayyaci shugaban kotun da takwaransa na Babbar Kotun Jihar Kano kan umarnin da suka bayar masu karo da juna kan shari’ar Sarautar Kano mai cike da rudani.