✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki rabu da amosanin ka

Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata.…

Mata da dama suna fuskantar matsalar amosanin kai. Musamman idan sun je unguwa ko gidajen biki, sai a ga suna ta soshe-soshe kamar masu kwarkwata. Wasu kuma sukan je shagunan wanke kai domin a magance musu wannan matsalar. Albishirinku ’yan uwana! Yau na kawo muku hanyar sauki da za ku bi don rabuwa da wannan matsalar amosanin kai. A ciki akwai ganyen kashu da lemun tsami da ruwan kwakwa da kuma kwallon mangoro.
Shin ko kun san cewa ganyen kashu na maganin amosanin ka? To, ga yadda za a sarrafa shi:
· A wanke ganyen kashu, sannan sai a daka shi a kwaba da ruwa.
·         Bayan hakan, sai a shafa a fatar kai a bari na tsawon rabin awa kafin a wanke. Za a iya yin haka har na tsawon sati biyu, inshaAllah, za a sami saukin amosanin ka.
Ko kun san cewa lemun tsami ma yana warkar da amosanin ka, musamman idan an hada shi da ruwan kwakwa?
·         A sami lemun tsami sannan sai a matse ruwan, sannan sai a hada shi da ruwan kwakwa.
· Sannan a shafa a fatar ka a jira na tsawon rabin awa kafin a wanke.
kwallon mangoro ma yana mangance amosanin ka. Kuma ana iya hada shi ne da madara ‘butter milk’ kamar haka:
· A bushar da kwallon mangoro, sannan a daka.
· Za a iya kwaba wannan garin kwallon mangoro da ruwa sannan a shafa a kai ko kuma da madara ‘butter milk’ sannan a shafa a fatar kai. Bayan minti 30 sai a wanke. Ana yi akai-akai, domin harkar fata sai a hankali ake samin sauki.