✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki magance zubewar gashin-kai

Sau da dama mata kan samu kansu cikin damuwa sakamakon zubewar gashin kansu, inda hakan ke faruwa a dalilin garin neman a gyara gashin, sai…

Sau da dama mata kan samu kansu cikin damuwa sakamakon zubewar gashin kansu, inda hakan ke faruwa a dalilin garin neman a gyara gashin, sai a bata, karshe gashin kai ya zube. Don haka ne na yi miki guzurin bayanin yadda za ki magance zubewar gashin-kai.
1 Amfani da mai: Ki samu daya daga cikin man gashin kai kamar su, Man Olibe oil da Coconut oil da Canola oil, sannan sai ki zuba daya daga cikin su a cikin tukunya, sannan ki dora a murhu. Ki bar shi ya yi zafi, amma ba wai sosai ko ya tafasa ba. Bayan kin sauke, sai ki shafa a gashin kanki. Yana da kyawu ki shafa a kofofin gashin kanki, hakan zai taimaka wajen sanya gashi ya yi tsawo da kuma sheki. Idan kin shafa sai ki rika gogawa da dan karfi-karfi. Bayan nan ki sanya hular ‘shower cap’ har zuwa awa daya. Daga nan ki shafa man shampoo. Bayan wani lokaci sai ki wanke kanki.
2 Amfanin da jus din citta ko tafarnuwa ko albasa: Ki samu albasa ko citta ko tafarnuwa, sannan ki markada daya daga cikinsu. Daga nan ki shafa a gashin kanki. Yana da kyawu idan kika shafa sai ki kwana da shi. Da safe ki wanke gashin kanki sosai.
3 Tausa a gashi: Idan kina tausar gashin kanki lokaci zuwa lokaci yakan haifar da gudanar jini cikin sauki a kofofin gashin kanki. Masana kiwon lafiya sun ce idan har jini na gudana yadda ake so a kofofin gashin kai, to hakan zai sanya gashin kai ya kara tsawo. Shafa man essential oil kamar su Labender da bay essential oil da almond da kuma sesame a lokacin da za a yi tausa na sanya gashin kai ya kara tsawo da kyawu da kuma sheki.
4 Amfani da abin da yake kashe kwayoyin cuta: Idan kina shafa abin da yake kashe kwayoyin cuta a gashin kanki zai hana shi zubewa. Misali ki samu ganyen shayin ‘Green tea’ biyu, sai ki jika su a cikin kofi daya na ruwan zafi. Bayan ya huce, sai ki shafa a gashin kanki. Idan kin yi hakan za ki bar shi har zuwa awa daya, daga nan sai ki wanke.  Ganyen shayin Green Tea yana dauke da sinadaran da ke hana zubewar gashi, a lokaci guda yana kara yawan gashin kai.