✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za ki gane miji nagari

daya daga cikin tanade-tanaden da ake yi wa tsarin auratayya shi ne neman aure, wanda yake da muhimmanci kwarai da ya kamata a lura da…

daya daga cikin tanade-tanaden da ake yi wa tsarin auratayya shi ne neman aure, wanda yake da muhimmanci kwarai da ya kamata a lura da shi tun farko.
A mafi yawan lokuta addinin Musulunci ya daidaita hakkokin da ke tsakanin namiji da mace, hakan ne ya sa namiji ke da ’yancin zabar macen da zai aura, kamar yadda ya ba namiji waccar dama, haka ita ma mace ya ba ta ’yancin zaben mijin da za ta aura, domin gudanar da zamantakewar aure tare.
    Matukar mace ta balaga kuma ta mallaki hankalin kanta, to tana da ’yancin zabar mijin da take so ta aura bisa radin kanta ba tare da an tilasta mata ba, amma wacce ba ta balaga ba, to iyayenta ne ke da ikon zaba mata mijin da za ta aura, abin da yake da muhimmanci a gare ki shi ne; ki zabi miji mai tsoron Allah, kada ki duba kyale-kyale na duniya.
Jikan Manzon Allah (SAW) Imam Hassan A.S ya ce “Aurar da ita (’yarka) ga mutum mai tsoron Allah domin in yana sonta zai girmama ta, idan kuma yana fushi da ita ba zai zalunce ta ba.
    Kamar yadda namiji idan ya ga mace zai iya cewa yana sonta, to haka ita ma mace ya halasta idan ta ga saurayi ko bazawarin da ya dace da ita, har ta ji tana sonsa, to ta yi kokari ta bayyana masa sonta ta hanyar da ta dace, sai dai akwai bukatar ki yi taka tsan-tsan da kuma amfani da hikima don gudun kada ki yi abin da zai zubar miki da kima, abin da aka saba da shi, shi ne namiji ya nemi auren mace, hakan daidai ne kuma abu ne da ya dace, to amma mace ma za ta iya ganin namiji kamili ta nuna kaunarta gare shi.
Ga wasu alamomi da za ki duba wajen gane miji nagari, wanda suka hada da: Tarbiyya da Ilimi da aiki da shi da yin sana’a da lazimtar addini da yarda da uzuri da kuma kawar da kai ga wadansu abubuwa.
Bayan an yi aure kuwa akwai alamomin miji nagari kamar haka: Tausayawa ga matarsa, rashin cutar da ita, nuna damuwarsa gare ta, kyautata wa iyali, yin hakuri, bayar da cikakkiyar kulawa da kuma kokari wajen neman halal.
Lallai dacen miji nagari abu ne mai muhimmanci ga rayuwar auren ’ya mace, domin da miji nagari ake samar da al’umma tagari da kuma gwaggwabar nasara mai karfi a zamantakewar aure. Abin a yi miki murna ne idan kin samu miji na kwarai. Domin samunsa na iya kai ki ga nasara da dacewa a duniya da gobe kiyama.
Ibrahim Hamisu Kabara ya rubuto daga Kano
Za a iya samunsa a wannan lambar: 08060651676