✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda za a sauya rigar Ka’aba a bana

Shugabannin Manyan Masallatan Harami sun mayar da bikin sauya rigar Ka'aba zuwa daren sabuwar shekarar Musulunci.

Shugabannin Manyan Masallatan Haramin Makka da Madina kasar Saudiya sun mayar da bikin sauya rigar Ka’aba zuwa daren sabuwar shekarar Musulunci.

A baya dai an saba yin bikin a ne safiyar ranar Arfa a watan Zhul Hijja, sai dai a bana za a gudanar da bikin ne a daren 1 ga watan Muharram 1444 baya Hijirar Annabi (SAW).

Wata sanarwa da aka wallafa fa Masallacin Harami ta babbaya cewa wannan sauyi ya fara ne sakamakon maida manyan bukuwan al’adu zuwa watannin da babu cikowar mutane.

Dalili na biyu shi ne kokarin kasar Saudiyya na karbar masu zuwa aikin Umarah daga ciki da wajen kasar a farkon shekara.

Sauya rigar Ka’ada, wadda ake kira da Kiswa, al’ada da a baya aka saba gani kowacce shekara a safiyar ranar Arfa.

A kan yi hakan ne a lokacin saboda a ranar babu babu alhazai a, sun tafi tsayuwar haka, don haka babu mutane sosai a Masallacin Haramin Makkah.

Hakan ke ba da damar a gudanar da aikin sauya Kiswa a tsanake, babu cunkoson jama’a.

Ka’aba ita ce alkiblar Musulumi a fadin duniya, inda daga ko’ina ake fuskantar idan za a yi sallah.

A yayin gudanar da aikin Hajji ko Umrah kuwa, akan gudanar da Dawafi ta hanyar zagaye ta sau bakwai.

Sabanin mai Umrah wanda zai yi dawafi daya, mai aikin Hajji, sau uku yake yin dawafi — Bayan isarsa Makkah, bayan jifa, da kuma kafin barin kasar Harami.

Msallacin Harami, mazaunin dakin Ka’aba shi ne mafi daraja a ban kasa.

Tarihi ya nuna Annabi Ibrahim (AS) tare da dansa, Isma’il (AS) ne suka gina dakin Ka’aba, shekaru aru-aru da suka gabata, bisa umarnin Allah.