✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a rage mutuwar mata masu ciki — Rotary

Wata kungiya da ba ta gwamnati ba, Rotary International, ta shirya taron horas da ’yan jarida kan dabarun fadakar da al’umma kan yadda za a…

Wata kungiya da ba ta gwamnati ba, Rotary International, ta shirya taron horas da ’yan jarida kan dabarun fadakar da al’umma kan yadda za a rage yawan mace-macen mata masu juna biyu da kananan yara.

Taron bitar da ke gudana Jihar Gombe, ya mayar da hankali ne kan ilmantar da ’yan jarida daga kafofin yada labarai na cikin gida da na waje kan hanyoyin fadakar da al’ummar yadda za a rage wannan matsala.

A jawabinta ga mahalarta taron na kwanaki uku, jami’ar kungiyar Rotary, Mary Alaje, ta bayyana cewa babban burin kungiyar shi ne inganta lafiya da walwalar mata da kananan yara da matasa a Najeriya.

Mary Alaje, ta kuma bayyana cewa taron horaswan na daga cikin kokarin da Rotary na rage mace-macen mata da kananan yara ta hanyar ilmantar da ma’aikatan yada labarai yadda za su isar da sako ga jama’a yadda ya dace.

Don haka ta jaddada muhimmancin bitar wajen ganin an rage matsalar.

Shi ma Kwamishinan lafiya na Jihar Gombe, Dokta Habu Dahiru, yaba wa kungiyar ya yi bisa shirya taron a lokacin da ya dace Kuma a kan lokaci.

Dokta Habu Dahiru, ya bayyana muhimmancin bayar da rahoto mai inganci wajen bunkasa shirye-shiryen kiwon lafiya, inda ya jinjina wa Rotary na zabo ’yan jarida da domin isar da sako ta yadda ya dace domin al’umma su a fahimce shi daidai.