Tafin kafarmu na daya daga cikin abin da ya kamata mu rinka kulawa da shi. Domin kuwa idan ba a yi hanzari an magance matsalar kaushin kafa ba, shi ne yake zarcewa zuwa faso.
Ta yaya mutum zai gane cewa yana da kaushin kafa? A lokacin da ya fara jin tafin kafarsa na janyo audugar jikin kujerar daki ko kuma yana kama kaya ko yana bata jikinka, wannan shi ne kaushin kafa.
- A karon farko a tarihi, za a fara rabon gado da mata a Jihar Ribas
- ‘Ambaliya ta yi ajalin mutum 134 da dukiyar N1.5trn a Jigawa’
Mutane da dama na son rabuwa da wannan matsala, don haka shi ne na kawo muku hanyoyin da za a bi don rabuwa da wannan matsala.
- A samu ruwan dumi sai a zuba a robar wanka sannan a saka kafar a rufe ta dan jiku kadan. Sai a ajjiye tawul a gefe.
- Bayan tafin kafar ya jiku, sai a cire daga ruwan dumin. Sannan sai a dauki dutsen goge kafa sai a goge inda kaushin yake. Sannan a sake mayar da kafar cikin ruwan dumi.
- Bayan minti kamar 15 sai a sake goga tafin kafar da dutsen goge kafa domin cire fatar da ta mace a tafin kafar.
- Sannan a wanke tafin kafar da sabulu a cikin ruwan.
- Sai a cire kafafun a goga su a jikin tawul domin su bushe.
- A samu man tafin kafa a shafa a tafin kafar, in ba a da shi ko man ‘Vaseline’ za a iya amfani da shi. Sannan a samu leda a sanya kowace kafa a ciki tare da sanya safa a tafin kafar sannan a kwanta barci da daddare.