✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda za a magance furfura

A kodayaushe mukan yi shafukan kwalliya domin matasa. A yau muna so mu tabbatar wa iyayenmu cewa, a harkar ado su ma ba a bar…

Man zaitun a kwalbaA kodayaushe mukan yi shafukan kwalliya domin matasa. A yau muna so mu tabbatar wa iyayenmu cewa, a harkar ado su ma ba a bar su a baya ba. Idan tsufa ta zo, gashin mutum kan zama fari sakamakon zuwan furfura. Wasu kuma halitta ce ba wai tsufar sukayi ba. Mun kawo muku hanyoyi da dama wadanda za a bi don magance furfura domin samun bakin gashi mai sheki.
·       Za a iya wanke gashi da man shampoo mai dauke da nau’in aloe bera . Yin hakan na dada karfin gashi da kuma sanya shi baki.
·        Za a iya amfani da lalle a gashi don magance furfura. A yi amfani da asalin lalle na gargajiya sai a hada da kofi (coffee) na shayi da kuma man zaitun. Ko kuma za a iya tafasa ganyen shayi sai a kwaba shi da lallen kafin a shafa a gashi. Sai a wanke gashi bayan awa daya.
·        Idan ana so gashi ya yi baki sosai to kada a sanya kofi, wato a hada lallen da konanniyar tafarnuwa. Idan an yi amfani da wadannan hanyoyi, za a ga canji domin ba shi da wani illa ga gashi