An samu barkewar yamutsi a Majalisr dokokin Saliyo, yayin da ake rantsar da sabbin ’yan majalisa bayan zaben shugaban kasa da aka yi a watan da ya gabata.
Mambobin jam’iyyar All People’s Congress (APC) ne suka kawo cikas bayan da aka nemi wadansu daga cikinsu da yawansu ya kai 16 a kan su fita daga zauren majalisar bayan sammaci da wata kotu ta gabatar akansu kamar yadda BBC ta ruwaito.
Al’amarin ya tabarbare kuma an kasa shawo kansa duk da cewa akawun majalisa ya dakatar da zaman majalisar na takaitaccen lokaci.
Sai da aka tura jami’an ’yan sanda cikin zauren majalisar domin su shawo kan lamarin.
An yi amfani da karfi wajen fitar da wadansu daga cikin ’ya’yan jam’iyyar APC.
Jam’iyyar APC ita ce ta fi yawan mambobi a majalisar dokoki amma ta sha kaye a hannun Julius Maada Bio na jamiyyar Peoples party a zaben shugaban kasar Saliyo da aka yi.
A farkon watan Afrilu ne aka rantsar da Mista Julius Maada Bio, a matsayin sabon shugaban kasar Saliyo bayan ya lashe zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.