✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ’yan bindiga suka kashe mutum 51 a Kaduna

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a kauyuka hudu da ke cikin Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda…

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kai wani mummunan hari a kauyuka hudu da ke cikin Karamar Hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda suka kashe akalla mutum 51 yayin da suka raunata wasu da dama.

Kauyukan da aka kai harin sun hada da: Kerawa, Zareyawa da Marina duk a cikin garin Kerawa.

Maharan sun kai harin ne da misalin karfe 6:00 na safiyar ranar Lahadi, bayan jama’ar garin sun dawo sallar asubahi.

Aminiya ta samu rahoton cewa, an kone gidaje da dama sannan ‘yan bindigar suka kwashe kayan abincin mutanen da suka raunata.

Kansilan mazabar Kerawa, Malam Dayyabu Kerawa, ya tabbatar da aukuwar harin.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ASP Mohammed Jalige, ya ce  jami’an ‘yan sandan sun samu rahoton harin kuma sun tuntubi babban jami’in ofishin Karamar Hukumar don yin binciken.

ASP Mohammed, ya kara da cewa, da farko sun fara samun rahoton kashe mutum 37 a ranar Lahadi, amma daga bisani adadin ya karu.