✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (5)

Wani kuma ya ce, sun amsar masa Naira dubu dari bakwai.

A shekarar 2012, shekara goma ke nan cur da ta gabata, wani al’amari mai ban mamaki ya faru da ni GIZAGO (08065576011), inda na gana da wata ‘aljana’ mai suna Ummulhairi da kuma mahaifinta.

Na zabi in ba ku labarin dukkan yadda ganawar tamu ta gudana, domin akwai gargadi da darussa masu yawa da za mu iya amfani da su a zamanance.

A yau in sha Allahu za mu karkare wannan labari, inda za mu tsakuro kadan daga labarin wasu da suka fada komar irin wadannan mutane ’yan damfara. Da fatan za mu dauki darasi tare da kiyayewa, amin!

A sakamakon wannan labari da na ba ku, wasu sun bugo waya, wasu kuma sun yo tes, suna sanar da ni cewa, su ma wadannan mayaudaran sun tuntube su.

Wani ma ya gaya mani cewa, har sun yi nasarar amsar Naira dubu dari biyar daga hannunsa. Wani kuma ya ce, sun amsar masa Naira dubu dari bakwai.

Don haka a yi hattara. Allah Ya kiyaye, amin.

Ina yi wa wadannan mutane da suke damfarar mutane nasiha da su ji tsoron Allah, su daina cutar jama’a, musamman ma yadda suke amfani da ilimin addini da Allah Ya ba su.

Su ji tsoron Allah! Ya ku masu bibiyar wannan shafi, ina kira da jan hankalinku cewa, duk wanda aka buga sunansa da lambarsa a jaridar nan, ya san da sanin cewa akwai ’yan damfara da ke zambatar mutane.

Za ka ji sun kira ka, su nuna cewa, ko dai su malamai ne ko kuma su nuna cewa su aljanu ne, za su taimaka maka.

Wasu ma za ka ji sun ce su manyan ma’aikatan gwamnati ne ko kuma hamshakan ’yan kasuwa, za su yi maka hanyar da za ka samu kudi ko babban aiki a Gwamnatin Tarayya.

Don haka a yi hattara, kada a sake a amince da irin wadannan mutane. Allah Ya kiyaye amin.

Na samu sako daga Badamasi Umar Gwada mai doya daga Jihar Neja, wanda ya ce: “Assalamu alaikum Gizago, da fatan kana lafiya.

“Ni ma aljanarka ta kira ni yanzu da lambar MTN dina da aka taba bugawa a shafinka kwanakin baya.

Saboda haka, yanzu ta ce in kira ta da karfe hudu na yamma. Duk yadda muka yi da ita zan kira ka in gaya maka.”

Sai Malam Sanusi Sani Dala ya aiko da cewa: “Salam Gizago, ina yi maka fatan alheri a haduwarka da aljanarka.

Don Allah wannan lambar ta yi kama da ta aljanarka 08065582543?

“Domin an kira ni da ita kuma mace ce, ta kama sunana radau kuma wai za ta fadi mani wata addu’a. Allah Ya kare mu daga dukkan abin ki, amin.”

Shi kuwa Lawal Ahmad, a nasa sakon, yana cewa: “Salam Gizagawa da sauran makaranta wannan jarida tamu mai farin jini.

“Zan ja hankalinmu ne game da wani sabon salon damfara da wasu makiya Allah suka fito da ita. Za a kira mutum da waya, da zarar ka dauka sai a fara kawo maka ayoyin Alkur’ani da hadisai.

“Sai a ce ka yi sadaka da dabino guda 11. In ka yi sadakar sai ka sake kiran su. To, daga nan su kuma sai su ce maka za su yi maka rokon Allah da saukar Alkur’ani kuma za a yi yanka.

“Daga nan za su bukaci ka turo da abin yanka ta katin waya, kamar na Naira dubu 10 ko 20. To daga nan ba za ka kara jin su ba.”

Shi kuwa Iro Kano, cewa ya yi: “Malam Gizago, barka da warhaka kuma na karanta jaridar Aminiya yau.

“Ka san Allah, ’yan damfara ne. Haka na yi wa wani aikin wutar lantarki, ya yi mani irin kalaman da ta yi maka.

“Daga karshe sai da ya amshe mani kudin da na yi masa aikin gida sukutum.”

Daga Lawal Ambasada Galadimawa Giwa: “Na karanta labarinka da aljana kuma ni ma abin ya faru da ni kuma har ma na dauki muryarta.

“Abin ya faru a ranar 28/4/2012. Don haka, in kana so ka turo mani da lambar da zan kira ka in ba ka labarin yadda muka yi da ita. Ni ma a jaridarku ta ga lambata.”

Abdul’aziz Kassim Abuja yana cewa: “To, Malam Gizago, sai mu ce Allah Ya kara tsare mu da irin wadannan mutane, domin ni ma kamar yadda ta faru da kai, haka ta faru da ni, amma ni nawa namiji ne ya kira ni, wai in samu dabino in yi sadaka da shi, da dai sauransu.

“A lura da duniya dai!” Hassana Usman Legas ta bayyana cewa: “Gizago, barka da warhaka. Shin da gaske ne ka hadu da aljannu ko labari ne kawai don nishadantarwa?”

Daga Sirajo M. A. Ruhogi Kaduna: “Assalamu alaikum. A gaskiya ina son shiga wannan kungiya ta Gizago, domin a kowane lokaci ina tare da ku. Don Allah a yi mani rijista.

“Kuma game da labarainka na aljana, kada fa ka yi wauta, domin a haka ake barin dami a kala. Ka ba wannan mata uzuri, ka ga rawar da za ta taka, don ba duka ba ne mayaudara.”

Wani bawan Allah kuma ya aiko sakon cewa: “Assalamu alaikum. Labarin aljana Ummulhairi na yau Juma’a ya ja hankalina matuka.

“Don Allah ku ba ni lambar wayarta, domin labarin ya yi kama da nawa, amma ni sunan aljanar Gimbiya, mai lambar waya kamar haka: 07066472269. Ina so in tabbatar ’yan damfara ne. Ku huta lafiya.”

Sulaiman Ibrahim KetuLegas yana cewa: “Assalamu alaikum Gizago, ina neman shawararka yanzun nan, domin halin da kake ciki na shiga, amma ni uban ne yake magana kuma ya ce in yi hadaya da rago yanzun nan. Ina neman shawara yanzu, don Allah.”

Salim Abubakar Bauchi yana cewa: “Assalamu alaikum Gizago, ni ma an yi mani wannan abin da ya faru da kai, wallahi. Allah Ya kiyaye dukkan masoya Aminiya da sauran al’umma daga sharrin wadannan ’yan damfara, amin.”

Shi kuwa Idris Shehu Abuja, cewa ya yi: “Assalamu alaikum Gizago. Wato yau na karanta labarinka game da aljana, wallahi na yi farin ciki, domin ka sosa mani inda yake mani kaikayi.

“Wallahi wannan labarin da ka fada, ya faru da ni ko kuma in ce ma yana faruwa da ni yanzu haka; domin akwai wasu abubuwan al’ajabi da suka faru da ni ta waya, amma zan so ka ba ni lambar waya mu yi magana, domin na tabbatar labarina zai taimaka maka, kuma za ka kara tabbatar da sharrin wadannan mutane da ke kiran kansu da aljanu.”

Daga Ummi Salma: “Malam Gizago, shin da gaske aljana ce ko dai wata ce take son yaudararka? Don Allah ka ganar da ni in sani.”

To jama’a, wadannan su ne kadan daga cikin sakonnin da na samu dangane da wannan labari.

Sauran dinbin mutanen da suka aiko da sakonni sai su yi hakuri, kasancewar ba mu samu damar bugawa a nan ba.

Muna rokon Allah Ya kiyaye mu daga fadawa komar ’yan damfara da sunan aljanu, amin.