✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (4)

Da na je, kila da na yi ido biyu da ‘aljani’ cikin siffar Danfulani.

A shekarar 2012, shekara goma ke nan cur da ta gabata, wani al’amari mai ban mamaki ya faru da ni GIZAGO (08065576011), inda na gana da wata ‘aljana’ mai suna Ummulhairi da kuma mahaifinta.

Na zabi in ba ku labarin dukkan yadda ganawar tamu ta gudana, domin akwai gargadi da darussa masu yawa da za mu iya amfani da su a zamanance.

A yau za mu dora daga inda muka tsaya, ku biyo ni!

Na ce masa na ji kuma na dauka. Sai ya ce mani: “Yauwa dana, haka nake son in ji. To ka kara saurare na.

A yau din nan zan tafi Harami, ka fada mani bukatunka guda uku kwarara, zan rubuta sunanka a wani allo da ke cikin dakin Ka’aba, in sha Allahu dukkan bukatun nan naka za su biya.

Na biyu, kamar yadda muka yi magana da diyata, ta ce ta amince da kai, don haka na ba ka ita aure, ta zama taka har abada amma ka saurare ni, zan gaya maka abin da za ka biya, a matsayin sadaki.”

Yana kawowa nan, sai dariyar da ta cika mani ciki ta kusa bayyana fili. Don haka sai na yi sauri na katse wayar.

Na yi ta sheka dariya ni kadai. Idan ba jahili ba, wane dan Adam zai amince ya auri aljana?

Gizago kuwa ba jahili ba ne, domin kuwa ya san cewa aljanu ruhi ne ba jiki ba. Babu yadda za a yi mutum ya auri aljana, sai dai a tatsuniyar Gizo da Koki.

Ni kuwa a raye nake, dan Adam ne ni. Don haka ba zan auri kowa ba sai ’yar Adam, ido-na-ganin-ido.

Ina cikin wannan kai kawo na tunani da dariya, sai wayata ta buga. Da na duba sai na ga lambar ‘aljana’ ce ta bugo. Na kuwa dauka. Da na ji muryar Baba sai na ba su hakuri, cewa netwok ne ya katse mana zance.

Don haka sai ya ci gaba da magana, ya ce mani: “Yanzu-yanzu zan tafi Saudiyya, da zarar na isa, zan kira ka da lambar waya, za ka ga cewa ta can ce.

“Sai ka kira ni, ka gaya mani bukatunka guda uku, domin in rubuta sunanka a allon nan na Ka’aba.”

Yana gama fadin haka sai ya kashe wayar. Bayan kimanin minti biyar, sai na ga an kira ni da wata lambar waya, wacce ke nuna cewa daga Saudiyya ne aka bugo.

Na dauka sai na ji muryar Baba, na dauka zai bari in fada masa bukatun nawa, sai ya ce mani: “Ka bugo wannan lambar, yanzu haka ina cikin Harami, sai ka gaya mani bukatun naka.”

Ni kuwa kawai sai na share shi, na ki bugawa. Domin babu maganar ma da ta kara bata mani rai kamar wannan.

Wai zai rubuta sunana a allon dakin Ka’aba! Ko wa ya gaya masa akwai wani allo da ake rubuta jerin sunayen masu neman bukata a wurin Allah?

Bai san cewa mun dade da sanin wane ne Allah ba? Allah ne fa Ya sanar da mu cewa Yana kusa da bawanSa fiye da yadda bawa ke kusa da jijiyar wuyansa, kuma Yana jin addu’ar mai addu’a, kuma Yana amsawa daga ko’ina aka kiraye shi.

Ni da na san haka, yaushe zan jira sai wani gaulan aljanin karya ya kai sunana dakin Allah?

Allah dai Ya kiyashe mu da aikin jahilci! Bayan kamar minti bakwai, sai kuma aka bugo mani da wata lamba ta Najeriya.

Da na dauka sai na ji muryarsa ce dai. Ya gaya mani cewa har ya gama abin da yake a Saudiyya, ya dawo.

Ya yi ta yi mani fada, wai me ya sanya ban kira shi ba. Na ce masa na kira amma wayar ta ki shiga.

“To shi ke nan, na roka maka abu uku. Na farko dai na roki Allah Ya albarkaci aurenku da diyata da na ba ka, Ummulhairi.

Na biyu, na roki Allah Ya dora ka kan Ministan Abuja, za ka samu arziki ta hanyarsa mai yawa.

Na uku, na roki Allah Ya yi maganin makiyanka.”

“Na gode, na gode Baba, Allah Ya saka da alheri!” Abin da na gaya masa ke nan.

Shi kuwa sai ya yi sauri ya ce to in saurara zai gaya mani abubuwan da ake bukata, domin sadaka da kuma kudin sadakin da zan biya.

“Dana Gizago, ka san gobe Juma’a ko? To da sassafe, ka sayi rago ka yanka, ka raba naman sadaka.

Ka tanadi Naira dubu dari biyu da hamsin, ka sanya cikin bakar leda, ka hada da turaren da ka ce ka saya mani.

“Ka je babban Masallacin Juma’a na Abuja da su. Da zarar an gama Sallah, ka bude wayarka, dana zai kira ka, zai tsaya a bakin babbar kofar masallacin ta yamma, sai ka ba shi sakon zai kawo mani.

Kada ka ji tsoro, zai zo maka a siffar kyakkyawan Bafulatani ne, domin ka san muna rikida.

“Kudin nan, su ne sadakin ’yata, za mu yi sadaka da su ne. Da zarar ka biya sadakin, zan gaya maka ranar da za a daura auren.

“A Saudiyya za a daura, kuma za mu tafi da mutanenka can gaba daya.”

“Allah wadaran naka Ya lalace!” Kalaman da na furta ke nan ni kadai, bayan mun kammala magana da aljanun karya.

Ni kuwa na so a ce na je Babban Masallacin Abuja, kamar yadda ya ce amma sai aka yi rashin sa’a, ba na garin Abuja a ranar, domin kuwa na je kauyenmu hutun karshen mako.

Da na je, kila da na yi ido biyu da ‘aljani’ cikin siffar Danfulani (Makaryatan banza)!!

Masu karatu, kun ji fa yadda wadannan mayaudara ke zaluntar mutane.

Kodayake suna amfani da lambobin waya daban-daban, bari in kawo maku lambobin da suka kira ni da su.

Shi Baba, ya rika kira na da wadannan lambobin: 08106201977, ta Saudiyya kuma ita ce: +009966501574583.

Ita kuma Ummulhairi, ta rika kira na da wannan lambar: 07066067157.

Za mu kammala