✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ta kwashe tsakanina da ‘aljana’ Ummulhairi (2)

Me ya sanya ta yi batun cuta, idan dama can babu nufin haka a zuciyarta?

A cikin shekarar 2012, shekara goma ke nan cur da ta gabata, wani al’amari mai ban mamaki ya faru da ni GIZAGO (08065576011), inda na gana da wata ‘aljana’ mai suna Ummulhairi da kuma mahaifinta.

Na zabi in ba ku labarin dukkan yadda ganawar tamu ta gudana, domin akwai gargadi da darussa masu yawa da za mu iya amfani da su a zamanance. Ku biyo ni!

Jama’a, idan kuna biye da ni, a wancan karo na tsaya ne daidai lokacin da ‘Aljana’ ta sake kira na, bayan ta jira na tsawon lokaci ban kira ta ba, kamar yadda ta ummurce ni da in yi.

Lokacin da ta kira ni, bayan na dauki wayar sai ta fara da cewa: “Assalamu alaikum, Malam Gizago.” Ni kuwa na amsa mata, har ma na kara da cewa: “Warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu.”

“Malam Gizago, ina fata ka aikata abin nan da na ce ka aikata!” Inji ta. Ni kuwa sai na ce mata a gaskiya ban aikata ba, domin kuwa ina jiran in kara samun bayani kafin in aikata.

Na ce mata maganar sadaka da kwafin Alkur’ani, akwai wani dan uwana da ya roki in saya masa kwafi daya, na dauki alkawari zan saya masa. Na ce, idan na dauki wannan a matsayin sadaka, ko ta yi?

“Kwarai kuwa, sadakar ta yi, don haka yanzu sai ka yi alwala, ka yi salatin Manzon Allah (SAW) guda goma sha daya. Kana gamawa sai ka kira ni.” Inji ta.

Har za ta kashe wayar, sai na yi sauri na ce mata, don Allah ki tsaya, kada ki kashe, zan so in yi maki wasu ’yan tambayoyi, amma ki taimaka ki amsa, mani, muddin dai kina son in ci gaba da sauraren ki.

“Babu damuwa, ka yi hakuri har sai ka aikata abin da na nemi ka aikata yanzu, ka daina yin garaje, za ka ji komai da kake neman ji game da ni da sauran zuri’ata.”

Tana gama fadin haka sai ta kashe wayar. Ni kuwa sai na sake shiga cikin tunani. Daga nan na gama tsara dukkan matakan da zan dauka, idan na sake jin muryarta, domin kuwa na sha alwashin ni dai ba zan kira wayarta ba.

Ban yi alwalar da ta ce in yi ba amma dai na yi wa Annabi salati, musamman saboda sanin fa’idar yin haka. Na yi amanna da hadisin da ke nuna matukar muhimmancin yi wa shugaban al’umma salati.

Allah Ya sanya mu zama cikin cetonsa a ranar gobe kiyama, amin. Ban dai kira matar nan ba har dare ya yi.

Mun kammala Sallar Isha’i, na shiga gida har na fara ’yan karance-karance na kafin in yi barci, can wajen karfe tara da rabi sai na ji wayata ta kada.

Ina dauka sai na ga lambar ‘Aljana.’ Da na dauka, bayan amsa sallamar da ta yi mani, ban bari ta fara magana ba, sai na tarbe ta da ban hakuri.

“Malama, don Allah ki yi hakuri, kin ji ni shiru dazu. Katina ne ya kare, kuma ban samu yaron da zai sayo mani ba. Shi ya sanya na kasa bugo maki.”

Da gangan na yi mata wannan karya, ba don komai ba sai domin dai in kara fahimtar wani abu daga gare ta.

“Malam Gizago, kada ka damu. Wannan ta wuce amma dai nan gaba ka yi kokari, duk abin da na ce ka yi, kada ka yi mani gardama.

Kamar yadda na gaya maka tun dazu, wannan abin alheri ne Baba ya umurce ni da in yi maka bushara.

Ga alama dai ba ka fahimci ko ni wace ce ba, kuma ba ka san wane ne babana ba, kila shi ya sanya kake sanyi-sanyi da al’amarinmu.”

Tana gama fadin haka, sai na yi sauri na ce mata: “Malama, ina rokon ki don Allah ki tsaya ki yi mani bayani dalla-dalla, yadda zuciyata za ta natsu.

“ Ki bari in yi maki tambayoyin nan da na ce zan yi maki dazu.”

Da gangan na yi mata wannan bayani. Matar nan sai ta amsa mani amma a wannan karon sai ta yi ta jero mani ayoyin Alkur’ani, tana yi tana fassarawa, tana hadawa da hadisan Manzon Allah (SAW).

Sai da ta dauki kimanin minti biyar tana haka, sannan ta bari na sake magana.

Na ce mata don Allah ta gaya mani sunanta, kuma ta gabatar mani da kanta, da manufarta zuwa gare ni. “Malam Gizago, ka saurare ni da kunnuwan basira.”

Ta fara magana. “Sunana Ummulhairi. Ina yi maka magana ne daga nan Hubbaren Mujaddadi Usman Danfodiyo, da ke Sakkwato.

“Muna tare da Baba ne, tun dazu yana yin wani aiki ne, idan ya gama zan hada ka da shi ku gaisa.

“Ina son ka gane cewa ni ba mutum ba ce, ni Aljana ce amma ba muguwa ba, ni ba arniya ba ce, musulma ce ni. Da ni da babana, muna dauke da alheri ya zuwa gare ka.”

Tana fadin haka sai na kyalkyace da dariya, duk da cewa ban kyakyata a fili ba. A lokaci guda kuma na ci gaba da sauraren ta.

“Baba yana bibiyar dukkan ayyukanka, ya lura da yadda kake jinkan tsofaffi. Watakila ka manta, akwai ranar da ka taimaki wani tsoho, ka ba shi wata sadaka.

“To shi tsohon nan bai mance da kai ba, don haka ya kudurci aniyar saka maka da mafificin alheri.

“Zuwa anjima kadan, zan hada ka da Baban, za ka ji muryarsa, sannan kuma zai sada ka da wasu abubuwan alherin.

“Yanzu sai ka yi salatin Manzon Allah guda goma sha daya, idan ka gama, daidai misalin karfe goma da rabi sai ka kira ni, lokacin nan ina sa ran Baba ya gama hidimarsa.”

Na ankara da cewa za ta kashe wayar, sai na yi sauri na tari numfashinta, na ce mata.

“A daidai lokacin nan kuwa yana da wuya in iya kiran ki, domin kuwa za mu je ganawa da Ministan Abuja, a kan wani muhimmin aiki da zai ba mu.

“Ina sa ran ma sai mun kai karfe daya ko fiye da haka. Don haka kada ki ji ni shiru.”

“Kada ka ji komai, koda karfe nawa ne, ka kira ni idan ka gama, babu wata damuwa.” Inji ta.

“Malama Ummulhiari.” Na kira sunanta da karfi, ina shirin sharara mata tawa karyar.

“Na’am! Malam Gizago.” Ta amsa kuma ta dan sarara domin ta ji abin da zan fada. Ni kuwa na ci gaba da magana.

“Ina yi wa Allah godiya da Ya hada ni da aljanun kirki irinku, ke da babanki, ko kuma in ce babanmu, domin kuwa daga yau na zama dan uwanku, abokin aminci da zumuncinku.

Yadda sunan nan naki ya kasance ‘Uwar Alheri’ Allah Ya sanya ki zama alheri a gare ni.

Bari ma in fito fili in gaya maki cewa, na ji a zuciyata cewa za mu hada zuri’ar alheri da ke. Ina fata dai ba ki da aure ko!”

Za mu ci gaba