A cikin shekarar 2012, shekara goma ke nan cur da ta gabata, wani al’amari mai ban mamaki ya faru da ni GIZAGO (08065576011), inda na gana da wata ‘aljana’ mai suna Ummulhairi da kuma mahaifinta.
Na zabi in ba ku labarin dukkan yadda ganawar tamu ta gudana, domin akwai gargadi da darussa masu yawa da za mu iya amfani da su a zamanance. Ku biyo ni!
- Yawan dalibai mata ya ninka na maza a Kano —Kwamishina
- Shugabannin Jami’o’i ba su da ikon bude jami’o’i —ASUU
Wata rana a cikin shekarar 2012, da maraice sakaliya, sai na ji wayata ta fara kuka, tana rera baitocin wakar: “Dare da yawa, rana da yawa za su zo gushewa, ga ruwan sama yayyafi, lokaci na damina zai yo wucewa…”
Ni kuwa sai karaf na dauka, na danna maballin amsawa, sai na ji wata kakkausar muryar mace, tana cewa: “Assalamu alaikum, Malam Gizago ne?”
“Wa’alaikumus salam warahmatullah. Ni ne, wa ke magana?” Na amsa sallamar, sannan na kara kasa hajar mujiya, da nufin jin mai wannan kira.
“Allah Sarki! Na san za ka yi mamakin jin muryata, ka ce wace tsohuwa ce wannan take kiran ka? To, kada ka yi mamaki da ikon Allah.
“Ba zan cutar da kai ba, na kira ka ne domin in yi maka albishir. Sai ka gode wa Allah…” Abin da ta ci gaba da fada mani ke nan, ni kuwa na ci gaba da saurare.
Matar nan da ta kira ni a waya kuma ta nemi kwantar mani da hankali, ba ta gabatar da kanta gare ni ba.
Bayan ta lura da cewa na natsu domin sauraronta, sai ta fara daure mani jiki da ayoyin Alkur’ani, sannan ta rika jawo hadisan Manzon Allah (saw) a kai-a kai.
Ta dauki kimanin minti biyar tana yi mani hudubobi. “Gizago, ka gode wa Allah,” inji ta.
“Akwai alherai da ke bibiyarka, za ka same su nan ba da dadewa ba, ba don komai ba sai domin yadda ka jajirce kana yi wa al’umma hidima, sannan kuma kana bautar Allah sau da kafa.”
Bayan ta dan saurara, ni kuma sai na yi tsam da raina, babu abin da nake yi sai tunani.
Na farko dai na fara tunanin cewa, to ita wannan mata, yaya aka yi ta san ni kuma wa ya gaya mata cewa wai zan samu wasu alherai? Ita wace ce? Wa ya sanar da ita ma wai ina yin ibada sau da kafa ga Allah?
Na so in yi mata wadannan tambayoyi amma sai ta katse ni da zance.
“Kada ka zama mai gaugawa. Gaugawa aikin Shedan ce. Idan ka lura, ina yi maka batutuwa ne da suke na alheri.
“Ina kafa maka hujjoji da ayoyin Alkur’ani da hadisan Manzon Allah (SAW).
“Ka san kuwa a matsayina na musulma, mai bin tafarkin Muhammadur Rasulullah, sallallahu alaihi wa sallam, ba zan cutar da kai ba da ayar Allah.
“Abin da nake bukata shi ne, ka kara saurare na, da sannu za ka kai ga biyan bukatarka.” Abin da ta gaya mani ke nan, a lokacin da na tambaye ta domin ta gaya mani ko ita wace ce.
“Idan kana tare da ni, bari in gaya maka wani abu da zai amfane ka.
“Yanzu-yanzun nan, ka samu kwafin Alkur’ani mai girma, ka bayar sadaka. Sannan kuma ka samu wani kwafin ka aje bisa shimfidar Sallah.
“Ka yi alwalla sannan ka kira ni, zan gaya maka sakon da Baba ya ce in shaida maka.” Abin da ta gaya manin ke nan, sai kawai ta ce “Wassalam.”
Ta kashe wayar, ta bar ni tsaye sototo, ina kai-kawo cikin tunani.
Bayan ta bar ni, sai na kara nitsawa cikin tunani, domin in kara tantance wannan al’amari mai daure kai. Daga nan sai na fara komawa cikin kalamanta, domin in kara samo manufarta.
Abu na farko da na fara nazari a kansa shi ne, inda ta ce: “Ka san kuwa a matsayina na musulma, mai bin tafarkin Muhammadur Rasulullah, sallallahu alaihi wa sallam, ba zan cutar da kai ba da ayar Allah.”
Kuma ga shi ta sake sako wani zancen, wai ‘Baba’ ne ya ba ta sako domin ta ba ni.
Shi kuma wane ne wannan Baban, a ina kuma ya san ni?
Nan take na tuno da wata almara, wacce take ba da labarin dila. Dila ne ya taho cikin daji, sai ya gamu da wani maharbi, ya ce masa: “Malam dila, ka bi wannan hanyar, kar ka bi waccan, akwai tarko.”
Shi kuwa dila sai ya ce: “Abin da babu shi, me ya kawo maganarsa? Don haka, na ma fasa tafiyar.”
Sai ya juya kawai ya koma inda ya fito, ya ki bin duka hanyoyin nan biyu da maharbi ya fada masa.
Don haka, da ta ce wai ba za ta cuce ni ba, sai na ce a zuciyata, to abin da babu shi, me ya kawo shi?
Me ya sanya ta yi batun cuta, idan dama can babu nufin haka a zuciyarta?
Abu na biyu da na sake tunanowa shi ne, labarin wani Sahabin Annabi (SAW), wanda Shaidan ya ba shi fatawa game da fa’idar Ayatul Kursiyyu.
Yadda abin ya faru shi ne, wata rana ne Shaidan ya canza siffa zuwa tsoho ya bakunci, Abu Hurairah (RA).
Ana kan haka sai shi sahabin ya kama shi yana yi masa sata, shi ne fa ya shirya masa karya amma ya rika hada shi da Allah don ya kyale shi.
Har ma ya gaya masa cewa idan yana so ya yi maganin Shaidan, to ya lizimci karanta Ayatul Kursiyyu.
Da ya gaya wa Manzo yadda abin ya faru, shi ne ya ce masa, Shaidan ne, abin da ya fadi game da fa’idar nan gaskiya ne amma game da uzurin da ya ba shi, shi makaryaci ne.
Da haka ne ni ma na fahimta da cewa lallai akwai wata munakisa a tare da matar nan da ta kira ni.
Na fahimta da cewa duk abin da ta gaya mani game da Alkur’ani da hadisan Manzon Allah, duk gaskiya ne amma dai duk da haka akwai karya cikin manufarta zuwa gare ni.
Haka kuma da na yi la’akari da labarin dila da maharbi sai na yanke hujjar cewa ba zan yi sadaka da Alkur’anin nan ba, domin kuwa tun farko ban yi niyya ba.
Kuma Manzon Allah (saw) ya ce mana kowane aiki yana tattare da niyya. Haka kuma, kamar yadda ta ce wai idan na kammala sadakar in kira ta, sai na ce ba zan kira ta ba.
Haka dai aka yi, ta jira domin in kira ta amma na kiya. Na dauka shi ke nan za ta kyale ni amma ina!
Kamar yadda na ce, wannan kira na farko da ta yi mani, ta yi shi ne a daidai misalin karfe hudu da rabi na yamma kuma da muka gama magana, na duba tsawon lokacin da ta dauka shi ne minti bakwai da sakan ashirin daidai.
Can wajen karfe biyar da rabi, sai na sake jin kira. Na duba mai kiran, sai na ga sunan ‘Malama.’ Domin kuwa bayan mun gama maganar farko, na ajiye lambarta da wannan suna.
Da na dauki wayar, kun san abin da mutunniyar nan ta gaya mani?
Ku biyo ni mako na gaba, in sha Allahu zan fayyace maku komai. Allah Ya kai mu lafiya, amin. Za mu ci gaba.