Daga hudubar Sheikh Waddah bin Yusuf Al-Jabaziy
Masallacin Al’urwatul Wuska, Depok, Indonesiya
Su a kullum suna wargaza al’umma da kawo tashin hankali da rudar da mutane da jirkita addini da hallaka mutane da kwace musu dukiya ko hakkokinsu, kuma suna umarni da abubuwan kyama, suna toshe hanyoyin isa ga abubuwa masu kyau.
Sukan bayyana alfasha da kwadayi da wauta a zantukansu, ga girman kai da jiji da kai da iya zakin baki. Allah Madaukaki Ya ce: “Idan suka yi magana sai ka saurara wa maganarsu.” Saboda iya zakin baki da sarrafa harrufa da karkata murya da fasaha a yayin maganar da dagewa kan zance da wasa da laffuza. Tirmizi ya ruwaito wani Hadisi da ke cewa: “Rashin magana da kunya wasu yankuna ne daga yankunan imani, amma yawan magana da rashin kunya wasu yankuna ne daga cikin munafunci.”
Daga cikin alamun munafukai: Akwai rashin karbar hukuncin Allah tare da riya cewa sun yi imani. Ciruwa zuwa ga hukuncin Allah yana tabbatar tsarki da tsabtar zuciya da mika wuya ga hukuncin Allah da ciruwa daga karkata da sha’awace-sha’awacen zuciya. Wannan kuwa bai samuwa a cikin zuciyar da munafunci ya yi mata hijabi. Saboda haka ne munafukai suka rasa wannan mika wuya ga Allah cikin hukuncinSa, kuma ba su neman yin hukunci da dokokin Allah a harkokinsu, sun fi fifita ra’ayinsu ko na wadansu a kan shari’a. Sai su rika bayyana girman Littafin Allah a baki, amma idan hukuncin Allah ya zo sabanin abin da suke so, sai su juya masa baya, su dage wajen yakar wanda ya bayyana musu wajibcin bin hukuncin Allah a kan kowane al’amari. Allah Ya yi gaskiya cikin fadinSa: “Suna cewa: “Mun yi imani da Allah da Manzon (Allah), kuma mun yi da’a.” Sannan wani yanki su juya baya daga cikinsu, a bayan fadin haka. Wadannan ba masu imani ba ne. Idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu, sai wani yanki daga cikinsu su kangare.”
Kuma saboda lalacewar zukatansu, ba su iya ba hukuncin Allah matsayin da ya dace, idan aka ga yau sun yi haka, to saboda wata maslaha ce da za su samu, ko ganima da za su kwasa. “Idan gaskiya ta kasance a gefensu, sai su zo masa suna masu kankan da kai. Shin a cikin zuakatansu akwai cuta ce, ko kuwa sun yi shakka ne, ko suna tsoron Allah Ya saukar da bala’i a kansu ne, ko ManzonSa ya fallasa su? Ba haka ba ne, wadancan mutane su ne azzalumai.” Sabanin masu imani da aka siffanta su da imani da samun rabo. “Abin sani kawai maganar muminai idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu, sai su ce: “Mun ji, kuma mun bi.” Wadancan su ne masu babban rabo. Wanda ya yi da’a ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsoron Allah, kuma ya yi maSa takawa, wadancan su ne masu rabauta.”
Daga cikin alamunsu akwai cewa: Ta cikin maganganunsu ana iya gane adawa ga ma’abuta gaskiya da salihan bayi. Sakamakon yadda zukatansu suke cike da kiyayya ga muminai, zukatansu suna nuna musu adawa. Duk da abin da suke boyewa a zukatansu ki da so, harsunansu sukan furta wani abu daga abin da suke boyewa. “Hakika kiyayya ta bayyana daga bakunansu, alhali abin da suke boyewa a zukatansu ne mafi girma. Muna bayyana muku ayoyin ne in kun kasance kuna hankalta.”
Abin da suka bayyana na kiyayya da mugun kulli da hassada, suna kokarin boye shi ta hanyar bayyana sabaninsa. Amma Allah Ya ki, sai Ya kunyata su ta hanyar abin da harsunansu suke fada a lokacin da suka fusata ko giyar daukaka da mulki ta buge su. “Shin wadanda suke da cuta a zukatansu suna zaton Allah ba zai bayyana mugun kullinsu ba ne?” Tabbas, duk mai basira zai gane su ta hanyar yadda suke magana da usulubinsu wajen furta magana.
“Da Mun so da Mun nuna maka su (munafukan), amma za ka gane su ta siffofinsu, kuma za ka gane su ta gazawa wajen magana. Kuma Allah Yana sanin ayyukanku.”
Wata alama da suka kebanta da ita kuma ita ce: Tsananin firgita a lokacin da wata fitina ta auku da rashin aminci a tare da su a lokacin da kasarsu ko al’ummarsu ke cikin tsanani. Su bayin duniya ne, ba su san su taimaka a kubuta daga bala’i ba. Ba ruwansu da nemo mafita, ba su yin wani yunkuri don sadaukar da kai ga kasa ko al’ummarsu. Shin irin wadannan mutane ne za mu yi mafarkin ce musu: “Al’ummarku, su saurari kira, ko mu ce, matasanku, kishi da son jama’a su motsa musu?”
Kada ka yi zaton wadannan munafukai masu raunin imani za su yi tsere ta yadda za su kasance cikin jarumai, kuma kada ka jira haduwa da su, ba don Allah Ya yi wa’adi da bayar da nasara da tabbatar da duga-dugan muminai ba, da babu abin da za su yi musu, face su kara musu shakka da rudu. “Kuma a lokacin da munafukai da wadanda a cikin zukatansu akwai cuta suke cewa; “Babu abin da Allah da MazonSa suka yi mana alkawari face rudi.” Kuma a lokacin da wata jama’a daga cikinsu suka ce: “Ya ku mutanen Yasrib (Madina)! Ba ku da wani mukami don haka ku koma.” Wani bangare daga cikinsu suna neman izinin Annabi (SAW), suna cewa: “Lallai gidajenmu wofintattu ne (ba masu kula da su,)” alhali kuma ba wofintattu ba ne, ba abin da suke nufi face gudu (daga jihadi).”
Bayan wannan tsoro da firgitar da suke tare da su, tunaninsu na nuna musu kamar mutuwa za ta shafe su. “Za ka ga wadanda a cikin zukatansu akwai cuta, suna kallonka, kallo irin na wanda magagin mutuwa ta lullube shi, to (mutuwar ce) mafi alheri gare su.”
Ka ji mamakin mutumin da zai jibince su, ya karfafa su, kuma ya daukaka su, alhali Allah Ya wulakanta su, kuma Ya bayyana halayensu. Ga Allah muke mika kukanmu!
Munafukai da cibiyoyin cutarwa: Daga cikin siffofinsu akwai kakkafa cibiyoyin cutarwa. A farkon Musulunci dai sun fake ne da kafa masallaci, wanda Allah Ya kira da ‘Masallacin Cutarwa.’ “Wadanda suka riki wani masallaci domin cutarwa da kafirci da rarraba tsakanin muminai da kare wanda ya yaki Allah da ManzonSa a gabani, za su rika rantsuwa cewa babu abin da muke nufi face kyautatawa. Kuma Allah Yana shaidawa su makaryata ne.”
Suna rantsuwar ba su nufin komai sai kyautatawa, idan ma’abuta gaskiya suka gina masallaci, su ma sai su gina masallaci, idan suka kafa wata cibiya, sai su yi hakan, idan suka ga za su kafa wani abin kirki, sai su rigaye su, duk wani abin alheri da suka yi niyyar yi, sai su ma su yi ko su rigaye su. Za ka ga munafukai suna kwaikwayon muminai ko suna gasa da su, ko suna bibiyarsu taki da taki, bisa zaton a amince cewa suna taimaka musu ko suna aiki irin nasu, alhali suna yin haka ne: “Suna yaudarayya da Allah da wadanda suka yi imani, sai dai ba su yaudarar kowa face kawunansu, amma ba su sani ba.” Saboda suna lullube karya da gaskiya.
Ina neman tsarin Allah daga Shaidan jefaffe. “Munafukai maza da munafukai mata, sashinsu da sashinsu suna umarni da abin ki kuma suna hana alheri, kuma suna damke hannuwansu. Sun mance Allah, sai Ya manta da su. Lallai munafukai su ne fasikai.
Allah Ya yi mana gafara baki daya.