✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Shugaba Buhari ya bunkasa harkar noma a Kebbi

A shekarar 2015 ne Gwamnatin Tarayya ta fito da shirin tallafawar manoman shinkafa da alkama da kuma waken soya ta yadda aka kudurta za a…

A shekarar 2015 ne Gwamnatin Tarayya ta fito da shirin tallafawar manoman shinkafa da alkama da kuma waken soya ta yadda aka kudurta za a samar da shinkafa da za ta iya ciyar da al’ummar Najeriya kuma ta samar da ton miliyan daya ga al’ummar kasar nan, a karkashin jagorancin Gwamnan Jahar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu. Ana tsammanin a shekara 2016 da 2017, Jahar Kebbi ta samar da shinkafar da ta zarce ton miliyan uku.

A ranar 17 ga Watan Nuwamba, 2015 ne Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi tattaki zuwa garin Zauro a karamar Hukumar Birnin Kebbi domin kaddamar da shirin noman shinkafa da alkama da kuma waken soya na rani da damina na shekara ta 2015 da 2016 a garin Zauro a Jahar Kebbi.

Shirin da shugaban ya kaddamar, wani shiri ne na musamman tare da hadin gwiwar Babban Bankin Najeriya a shirin wanda aka kira (ANCHOR BORROWERS) domin bayar da tallafin noma da kuma rage zaman kashe wando ga marasa aikin yi a kasar nan. Gwamnatin tarayya ta fito da wannan shirin ne domin ta farfado da arzikin da ke cikin noma a kasar nan, musamman bisa la’akari da tabarbarewar arzikin kasa, tare da rage yawan dogaro da arzikin man fetur.

Ganin irin amfani da cigaban da aka samu akan noman shinkafa da alkama da kuma waken soya a Jahar Kebbi, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nada Gwamnan Jahar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu a matsayin shugaban kwamitin gudanar da sha’anin noman shinkafa da alkama a Najeriya. 

Saboda haka Gwamnatin Jahar Kebbi a karashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta ga cewa ya zama wajibi ta fito da wannan tsarin noma domin maido da arzikin noma a Jihohin Najeriya, daga nan kuma ta bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da cewar ya shigo cikin wannan shirin kamar yadda shugaban kasa ya bada ummurni tun daga farko, don bayar da tasu gudunmuwa ta hanyar bayar da tallafin kudi da kayan noman ga manoman Jahar Kebbi.

Kwamitin da Shugaban kasa ya nada akan sha’anin noman shinkafa da alkama a karkashin Sanata Abubakar Atikutu a wancan lokaci, kwamishinan sa ya ziyarci jihohin da ke noman shinkafa da alkama domin ganin irin yadda za su iya ba da tallafi ga jihohin don kara bunkasa aikin noma a Najeriya. Hasali ma ya fito fili ya bayyana cewar burina shi ne inga ana sayar da shinkafar Kebbi a gidajen cin abinci a birnin New York na Amurka da Japan.

Haka ma Gwamnatin Bagudu ta gayyato wasu manyan ‘yan jaridun kasar nan da na kasashen waje da kuma cibiyar bincike ta kasa da kasa da ke garin Ibadan akan nazarin aikin noma na zamani da kuma cibiyar binciken aikin noma ta Lake Chad ta garin Maiduguri zuwa Jahar Kebbi don gane wa idanunsu irin gagarumin noman shinkafa, alkama da kuma waken soya da manoman jihar ke yi, inda ‘yan jaridar suka ga yadda al’ummar Jihar Kebbi suka rungumi noma gadan-gadan.

Ganin irin kokarin da Sanata Abubakar Atiku Bagudu ke yi wurin ganin cewa arzikin noma ya bunkasa a Jihar ta Kebbi da ma kasa baki daya, wasu kamfunan jaridun kasar nan suka ga ya dace su karrama shi da lambar yabo wanda shi ne dalilin da yasa Jaridar banguard da Leadership suka ba shi lambar yabo a matsayin Gwamnan da ya fi jajircewa wajen bunkasa noma a kasar nan, akan haka kuma kamfanin Jaridar Media Trust wanda ya ke buga Jaridar Daily Trust da Aminiya, ya shirya nuna amfanin gona tare da hadin gwiwar ma’aikatar aikin gona ta Jihar Kebbi, inda kamfanoni da dama suka sami halartar gaggarumin nuna amfanin gona wanda aka yi a Kebbi. 

Wani manomi Salihu Dila Kamba wanda ya ce sun godewa wannan Gwamnatin ta Sanata Abubakar Atiku Bagudu da ta samar masu da babbar kasuwar sayar da shinkafa a garin Kamba. Ya kara da yin kira ga al’ummar Dandi da su ci gaba da ba Gwamnatin Bagudu goyon bayan da ya kamata.

Har ila yau shi ma sarkin noman Jihar Kebbi, Alhaji Muhammadu Hakimi Jiga babban manomi a jihar kuma daga karamar hukumar mulki ta Aliero, ya ce idan gwamnatin Jihar Kebbi ta na jawo manoman kwarai kusa da ita domin ba ta shawarwari akan harkar noma, ya ce Jihar Kebbi na iya noma shinkafa da tafi nauyin ton miliyan uku duk shekara, domin Allah Ya albarkaci Jihar da kasar noman Shinkafa. Sannan Gwamnatin Kebbi karkashin jagorancin Sanata Abubakar Atiku Bagudu ta mayar da hankalinta wurin noma. Don haka ya ce, yana da tabbacin Jihar Kebbi na iya noman da ya wuce ton miliyan uku a shekara daya, amma in an nemi manoman kwarai sun bada shawara.

Ya kuma kara rokon manoman Jihar Kebbi da su kara zage damtse wurin noma don fitar da Jihar da Najeriya baki daya daga kungiya, ganin yadda Najeriya ta yi dogaro da Jihar Kebbi akan noma. Ya ci gaba da cewa mu dai manoma a Jihar Kebbi mun cigaba domin a shekarun baya idan ka yi noma sai ka rasa wanda zai zo ya saya. Amma yanzu don ka noma Shinkafar Naira Miliyan 100 Kamfanin Labana zai saye ta nan take cikin sa’oi hudu kudi sun shiga hannun ka.

A wannan rahoto na musamman da Aminiya ta gudanar, ta binciko cewa an fito da shirin ne don habaka kasuwancin bankuna ta hanyar bayar da tallafin noma, a kuma kara inganta kamfanonin da ke sarrafa abubuwan more rayuwa, da kuma habaka kasuwacinsu, a kuma samar da kudaden shiga ga gwamnatin tarayya. Su kuma manoma da kuma masu saye da sayar wa za su kara noma mai yawa da zai wadaci mutanen kasar nan.

daya daga cikin cigaban da harkar noma ta samu a Jihar Kebbi shi ne hadin gwiwa tsakanin Jihar Kebbi da ta Legas inda Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya yanke shawarar jawo daya daga cikin jihohin kasar nan don yin shiri na musamman kan hada kai domin kulla huldar kasuwanci akan amfanin gona. Daga bisani jihohin biyu suka amince da yin kawancen noman shinkafa ta yadda a ranar 23 ga Maris, 2016. Gwamna Sanata Abubakar Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da Gwamnan Legas Ambode suka rattaba hannu kan yarjejeniyar.

Wannan yarjejeniyar wata fitila ce aka haska ga sauran Jihohin Najeriya akan maida hankalin su wajen kasuwanci kan amfanin gona da ake nomawa a cikin kasar nan tare kuma da samar da ayyukan yi ga daruruwan mutane, a kuma rage zaman kashe wando ga wasu matasan kasarnan.

Wannan kawancen wata hanya ce aka fito da ita don karawa kasuwanci kwarin gwiwa da kuma kara samar da hanyoyin walwala da jin dadin al’ummar jihohin biyu da kuma farfado da arzikin kasa ta hanyar noma abincin da zai wadatar da mutanen kasar nan baki daya. Wannan hadin gwiwa tsakanin Jihar Legas ya samar da Shinkafa a babban kasuwar nan ta Legas da ake cewa (LAKE RICE). 

Haka zalika shirin noma a Jihar Kebbi na cigaba da samun nasarori, inda a cikin kwazon Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ya jawo masu zuba hannun jari ga harkar noma domin bada tasu gudunmuwa inda kamfanin sarrafa shinkafa na Labana Rice Mills ya kaddamar da katafaren kamfanin casar shinkafa a cikin garin Birnin Kebbi a cikin shekara biyu da wasu watanni da suka gabata, kuma a cikin shekara daya da ta gabata Gwamnatin Jihar Kebbi ta yi kokarin ganin ta bunkasa harkan naman shanu a Jihar ta Kebbi, kai har ma da irin kokari da Gwamnatin Nijeriya ke yi don ganin ta bunkasa harkar noma da kuma farfado da tattalin arzikin kasar, a bara mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya kaddamar da wani gagarumin aiki a Jihar Kebbi.

Aikin da aka kaddamar kuwa shi ne na bude kamfanin sarrafa shinkafa mafi girma a yankin Afrika ta Yamma, a karamar hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi mai suna “WACOT RICE MILLS” A jawabinsa na kaddamar da kamfanin, Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya ce noma da ma’adanai za su kasance daya daga cikin abin da Gwamnatin tarayya za ta baiwa fifiko har ta gama tsawon nata mulki domin noma da ma’adanai babu abin da ya fi su in dai zancen inganta tattalin arziki a ke yi.