✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda shirin sakin madatsar ruwa daga Kamaru ya jefa ’yan Najeriya cikin fargaba

Mutum miliyan 1.4 lamarin ya shafa a ambaliyar ruwan da aka yi a bara a Najeriya.

Gwamnatin Tarayya ta shawarci gwamnatocin jihohin da ke yankuna a sahun gaba-gaba da su dauki matakan da suka dace domin dakile illar da ka iya haifar da ambaliyar ruwa saboda bude Madatsar Ruwa ta Lagdo.

Ministar Harkokin Jin kai da Yaki da Fatara Dokta Betta Edu ce, ta ba da wannan shawarar a lokacin da take ba da sanarwar gargadin ambaliyar ruwa yayin taron Majalisar Zartarwa da Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a ranar Litinin.

Edu ta ce wannan kiran ya zama dole ne biyo bayan sanarwar da hukumomin Kamaru suka yi na sakin ruwa daga Madatsar Lagdo na kasar.

Ministar wadda ta yi jawabi a gaban Ministan Albarkatun Ruwa da na Muhalli, ta bayyana bukatar aiwatar da tsare-tsare masu inganci da ayyukan ceto da nufin dakile illolin ambaliya.

Edu yayin da take yaba himmar Gwamnatocin Jihohi wajen magance matsalolin gaggawa, ta bukace su da su tabbatar da kwashe ‘yan Najeriya da ke zaune a yankunan da ambaliyar ruwan za ta shafa zuwa wurare masu aminci.

Mazauna wasu yankuna da ake samun ambaliyar ruwa kusan duk shekara a Najeriya sun shiga fargaba sakamakon sanarwar yiwuwar bude madatsar ruwa ta Lagdo da hukumomin Kamaru suka yi.

Da ma duk shekara sai hukumomin Jamhuriyar Kamaru sun saki ruwan Madatsar Lagdo saboda tumbatsar da take yi, abin da kan janyo mummunar ambaliyar ruwa da ke shafar wasu jihohin Najeriya.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar da sanarwa a ranar 21 ga watan Agusta kan batun, bayan samun sako daga hukumomin Jamhuriyar Kamaru.

Bayan hakan ne hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta fitar da sanarwar cewa hukumomi na daukar matakan hana ta’azzarar lamarin, tare da jan hankalin al’umomin da abin ka iya shafa don daukar matakan da suka dace.

A Jihar Binuwai da ke yankin tsakiyar Najeriya ma, daya daga cikin jihohin da suka fi fuskantar bala’in ambaliyar sakin ruwan madatsar ta Kamaru, dubban mutane ne suka shiga fargabar abin da ka je ya zo na barnar da ambliyar za ta yi musu.

Sai dai duk da cewa a baya ambaliyar ta sha yi musu barna ta dukiya wani lokacin har da rayuka, Malam Yahaya ya ce a bana ma babu wani tanadi da suka yi na daukar mataki illa iyaka suna jiran abin da Allah da hukumomi za su yi.

Me ya sa ake sakin ruwan Madatsar Lagdo?

Madatsar Ruwa ta Lagdo na yankin Arewacin Jamhuriyar Kamaru ne kuma an fara gina ta a shekarar 1977 aka kammala a 1982, kuma tana da girman murabba’in kilomita 586.

Madatsar Ruwan na daga nisan kilomita 50 daga birnin Garoua a kan hanyar Kogin Binuwai.

An gina Madatsar Ruwan Lagdo ne don samar da wutar lantarki ga Arewacin Kamaru da kuma ba da damar yin noman rani na hekta 15,000.

Duk shekara a lokacin damina, ruwan sama kan sa Madatsar Lagdo ta tumbatsa ta yadda har sai an saki ruwan don gudun kada ya jawo wata mummunar barnar.

Idan har ba a saki ruwan nan ya kwarara ba, to hakika barnar da zai yi za ta ci yankunan Kamaru da yawa ta kuma ci mafi yawan sassan Najeriya tun daga Arewa har yankin Kudu maso Kudu wato Neja-Delta.

Sannan ginin nata ya biyo bayan yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kasashen Nijeriya da Kamaru ne bisa sharadin cewa kowace kasa za ta gina madatsa daya, ta yadda idan na Kamaru ya tumbatsa aka saki ruwan, zai tafi ya shiga Madatsar Ruwan Dasin da Nijeriya za ta gina a Jihar Adamawa don gudun samun ambaliya.

A lokacin yarjejeniyar, an sa ran ita ma Madatsar Dasin za ta samar da megawatt 300 na lantarki tare da ba da damar yin noman rani a fadin hekta 150,000 a jihohin Adamawa da Taraba da Binuwai.

Sai dai tun bayan cimma yarjejeniyar a shekarar 1982, har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta kammala gina Madatsar Dasin ba.

Hakan ya sa idan an saki ruwan Madatsar Lagdo maimakon ya shige Madatsar Dasin da aka yi niyya, sai ya malale ya shige Kogin Benuwe ya yi ambaliya a jihohin da ke da kogunan da suka hade da na Binuwai din.

Jihohin da sakin ruwan ke shafa

A lokuta da dama sakin ruwan Madatsar Lagdo kan janyo ambaliya da barna mai yawa a jihohin Nijeriya da dama.

A misali a shekarar 2022 kawai, sakin ruwan ya jawo barna mai yawa har da asarar rayuka da lalacewar dumbin gonaki da kadarori na biliyoyin naira a jihohi da dama, inda abin ya fi muni a Jihar Kogi.

A ambaliyar 2022 ta Najeriya, mutum miliyan 1.4 lamarin ya shafa a cikin jihohi 27, sannan mutum sama da 500 sun mutu yayin da gidaje kusan 90,000 ruwa ya shafe.

A 2019 ma an taba sakin ruwan ba tare da sanarwa ba, inda aka yi mummunar ambaliya a jihohin Adamawa da Taraba da Binuwai da Kogi da yankin Neja-Delta a watannin Oktoba da Nuwambar shekarar.

A bana kuwa, hukumomin Najeriya sun ce sakin ruwan ka iya jawo ambaliya a Adamawa da Taraba da Benuwe da Nasarawa da Kogi da Filato da Gombe da Bauchi da Anambra da Edo da Delta da kuma Bayelsa.

Hukumomi da al’umma na bukatar daukar matakai

A sanarwar da ta fitar, Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta ce hukumomin Kamaru sun sanar musu cewa za su bude kofofin Madatsar Lagdo da ke kan hanyar Kogin Binuwai.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya, a cikin sanarwar tata, ta ce tuni ta bai wa shugaban hukumar ba da agajin gaggawa ta NEMA umarnin daukar dukkan matakan da suka dace don rage tasirin abin da sakin ruwan ka iya jawowa.

Cikin matakan da ta umarci NEMA ta dauka din har da na wayar da kan al’ummomin da suke rayuwa a yankunan da abin zai shafa don su dauki matakan kariya.