✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda shirin ‘Dadin Kowa’ ke hana mata yin Sallar Asham

Iyaye da sauransu a Jihar Kano sun koka tare da nuna damuwarsu bisa yadda fitaccen wasan kwaikwayon na Dadin Kowa wanda ake haskawa a gidan…

Iyaye da sauransu a Jihar Kano sun koka tare da nuna damuwarsu bisa yadda fitaccen wasan kwaikwayon na Dadin Kowa wanda ake haskawa a gidan talabijin na Arewa24 ya ci karo da lokacin sallar Isha da asham da ake gabatarwa a lokacin azumi.

Shirin wasan talabijin din fitaccen wasan Hausa ne da ake haskawa a tashar talabijin din Arewa24 a duk ranakun Talata da misalin karfe 8:00 na dare, sannan a maimaita shi a ranakun Asabar da misalin karfe 8:00 na dare.

Wasu daga cikin iyayen sun bayyana damuwarsu bisa yadda lokacin haska shirin ya ci karo da lokacin sallah, wanda hakan yake hana yara da ’yan mata mayar da hankali wajan gudanar da ibadunsu a cikin wannan wata me falala na Ramadan da ke bukatar Musulmi ya dukufa wajen ibadunsa.

Iyayen sun yi kira tare da mika bukatarsu ga hukumonin gidan talabijin da sauran masu ruwa da tsaki a harkar da su yi kokari wajen ganin an canja lokutan haska shirin wanda hakan zai taimaka wa yara kanana da ’yan mata su samu damar mayar da hankalinsu wajen gabatar da ibadunsu a cikin wannan wata mai albarka, sannan su dawo kallo shirin.

Daya daga cikin iyaye, wacca ta bayyana kanta da suna Hajiya Amina Sunusi, ta nanata cewa akwai bukatar canja lokacin, sannan ta yi kira da a duba lamarin bisa irin illar da wannan shirin ke haifar wa musamman a cikin wannan wata mai falala ya kama hanyar karewa.

“Lallai ya kamata iyaye su mayar da hankali wajen lura da yaransu tare da tabbatar da cewa sun mayar da hankalinsu wajan gabatar  da ibadunsu.

‘Ibadar ta fi nishadi’

“Za mu yi farin ciki matuka idan shuwagabannin wannan talabijin din za su duba lamarin yuwuwar canja lokutan haska shirin wasan musamman a cikkn wannan wata na Ramadan.

Nishadi yana da muhimmanci amma gudanar da ibada ya fi muhimmanci sama da komai.

Wannan shirin wasan talabjin din yana hana yara zuwa Masallaci domin aiwatar da ibadunsu wanda kuma a matsayinmu na iyaye hakki ne akanmu da mu tabbatar da cewa yaranmu sun taso akan tarbiyar irin ta addinin Musulunci.”

‘Kora yaran nake yi zuwa Masallaci’

A bangare daya kuma, Alhaji Ali Muhammad wanda yake shi ma uba ne da ake kallon shirin a gidansa cewa ya yi, “lokuta da dama sai dai in kashe talabijin din in kora su zuwa masallaci.

Suna ba shirin talabijin din lokaci da muhimmanci fiye da yadda suke bai wa sallolin Isha da Tarawihi muhimmanci a wannan wata na Ramadan.”

Alhaji Ali ya kara da cewa, “duk ranakun Talata da Asabar yara suna gujewa zuwa Masallaci domin gudanar da ibada wanda hakan yana da alaka da wannan shirin wasan Hausan na Dadin Kowa da ake haskawa.

A dalilin haka nake kashe talabijin din domin na tabbatar da cewa sun tafi sun gudanar da ibadunsu.”

‘Ba kowace tasha ake kallo ba a gidana’

A nata bangaren, Hajiya Ummi Bello, wadda ita ma ake kallon shirin a gidanta ta kara da cewa, “lallai iyaye ya kamata su mayar da hankali wajen lura da irin tashoshin talabijin din da kan iya dauke wa yara hankali wajen hana su ibadunsu.

“Ni kam ina yawan kulle wasu daga cikin tashoshin talabijin din da nake ganin za su iya zama barazana ga tarbiyar yarana da kuma shagalantar da su akan ibadunsu.”

‘Bai kamata a rika haska irin fina-finan ba a Ramadan’

Da yake jawabi kan lamarin, Limamin Masallacin Triumph da ke Jihar Kano, Mallam Lawan Abubakar ya kalubalanci lamarin tare da cewa lallai irin wadannan shirin wasan na Hausan bai kamata a rika haska su ba a cikin wannan wata na Ramadan duba da cewa wata ne mai falala da rahma da kuma tarin albarka.

Saboda ne ya ce ya kamata dukkan Musulmi su mayar da hankali wajen ibadunsu maimakon su shagala da abin da ba zai amfane su ba .

 “Mafi yawancin irin wadannan shirye-shiryen fim din, ba Dadin Kowa kadai ba, za a iya cewa ana shirya su ne a cikin watan Ramadan watawila a daidai lokacin sallah domin a shagalantar da Musulmi tare da dauke hankulansu daga gudanar da ibadunsu kamar yadda ake shirya wasannain kwallon kafa a irin daidai lokutan sallah wanda hakan shi ma yana hana Musulmi mayar da hankali wajen ibadunsu.

“Ya kamata Musulmi su sani cewa watan Ramadan wata ne mai cike da falala da tarin albarka da kuma neman gafarar Ubangji.

Wannan wata dama ce ga Musulmi domin su mayar da hankali wajen gudanar da ibadunsu domin su samu damar amfanuwa wannan wata mai albarka,” inji shi.

Abin da tashar Arewa24 ta ce Aminiya ta ziyarci gidan talabijin din na Arewa24 da ke Jihar Kano domin jin ta bakinsu kan wannan koke da bukatar iyayen kan shirin na Dadin Kowa, sai dai kuma duk kokarin da muka yi domin samun bayanin abin ya ci tura, inda wadanda wakilinmu ya gani a gidan talabijin suka bayyana cewa ba sa zantawa da manema labarai.

Sai dai wata majiya mai karfi daga cikin gidan talabijin din ta sanar da Aminiya cewa gidan talabijin din Arewa24 na haskaka shirye-shiryensu a kasashen ketare domin masu kallonsu da ke ko’ina a duk fadin duniya saboda haka ba zai yiwu ba su sauya lokutan wadannan shirin nasu na Dadin Kowa ba.

“Dole ba za mu iya sauya lokutan shirye-shiryenmu ba duba da cewa masu kallonmu na zaune a kasashe ne dabandaban,” inji majiyarmu din.

Majiyar ta kara da cewa, “babu wani shirin wasan talabijin da zai dauke wa masu kallo hankali har ya shagaltar da su zuwa ga barin ibadunsu, sai dai ko idan da ma mutum ba shi da niyyar ibadar.”