A ranar Talata ne Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya kaiwa tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ziyara domin ya jajanta masa kan rasuwar mahaifinsa wanda ya koma ga Mahaliccinsa a ranar Juma’a ta makon jiya.
Sarki Aminu ya ziyarci tsohon gwamnan ne a gidansa da ke kan titin Miller a Unguwar Bompai yayin da ake zaman makoki da karbar gaisuwa bayan kwanaki uku da rasuwar mamacin.
- An kashe ’yan bindiga 9 a hanyar Kaduna-Abuja
- Masar ta kulle masallaci saboda karya dokokin kariyar COVID-19
Mahaifin tsohon gwamnan kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Alhaji Musa Sale Kwankwaso, kafin rasuwarsa shi ne Makaman Karaye kuma Hakimin Madobi wanda ajali ya katsa masa hanzari bayan ya shafe shekaru 93 a doron kasa.
Sarkin yayin ziyayasa ta nuna alhini, ya bayyana mamacin a matsayin jakadan zaman lafiya, duba da irin gudunmawar da ya bayar ta fuskar wanzar da zaman lafiya a masarautar Kano lokacin da masarautar tana dunkule wuri guda.
Ya kuma bayyana mamacin a matsayin mutumin da ba za a taba mantawa da shi ba, inda ya yi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya ba ‘yan uwa da abokan arziki hakurin wannan rashin.
A nasa jawabin, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana godiyarsa ga sarkin na Kano bisa ziyarar ta’aziyyar da ya kawo masa.