✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Sarkin Hausawa ya kwantar da tarzoma a Legas

Mai martaba Sarkin Hausawan Ajeromi Ifelodun a Legas, Alhaji Adamu Abubakar Nebi ya shaida wa Aminiya yadda masarautar sa ta yi nasarar kwantar da wata…

Mai martaba Sarkin Hausawan Ajeromi Ifelodun a Legas, Alhaji Adamu Abubakar Nebi ya shaida wa Aminiya yadda masarautar sa ta yi nasarar kwantar da wata kura da ta taso a yankin karamar hukumar gundumar mulkinsa da kewaye, bayan da aka kashe wani barawo a yankin.

A cewar Sarkin Hausawan, ire-iren matasan nan ’yan daba da ’yan siyasa ke amfani da su a lokutan siyasa, su ne suke so su zame musu karfen kafa a yanzu, tunda lokacin siyasar ya wuce ba su da aikin yi sai zaman kashe wando su ne suka addabi mutanen yankin da sace-sace, ta yadda babu yadda mutum zai ajiye motar sa ba tare da an fasa gilashi an yi masa sata ba, su ne suke wabce wa mata jakukunansu na hannu da fasa rumfunan kasuwa suna sata, har ta kai ga sai su bi mutum har gida cikin dare su yi masa fashi da makami.
“Da muka ga wannan abin ya yi yawa don har ya kai ga matsalar na son cin karfin ’yan sanda sai muka je da maganar ga kwaminshinan ’yan sandan Jihar Legas, inda nan take ya kira shugabannin yankin kaf, waɗanda suka hada da shugabanin masarautun gargajiya da shugabannin ’yan kasuwa da manyan jami’an ’yan sandan yankin. Sannan ya ba mu shawarar mu hada kai da ’yan sanda mu nemi iyayen yaran nan mu zauna da su. Hakan ne ya sanya muka yi zama, sannan muka yi shiri da ’yan sanda da kungiyoyin ’yan sunturi aka yi ta kai wa dabar ’yan zauna garin banzan farmaki aka tarwatsasu,” inji shi.
A cewarsa wata matsalar da ta taso ne bayan mutuwar wani da ake zargin barawo ne da wasu ’yan sintirin Hausawa suka kama. Duk da cewa ba su suka kashe shi ba, don sun mika shi ne ga kungiyar Yarbawa ta OPC, inda ’yan uwan wannan mamaci suka yi ta yada barazanar daukar fansa. Hakan ne ya sanya shi zama da shugabanin yankin dama shugabannin tsagerun Yarbawan, inda suka tattauna suka fahimci junansu a fadar sa a ƙarshen makon jiya, har ta kai ga an samu fahimtar juna daidaito.
Sarkin Hausawan, wanda tsohon sojan ruwa ne ya shaida cewa kokarin da suka yi ne ya hana yaduwar tarzomar, domin da yawa daga cikin ’yan Arewa mazauna yankin har sun fara yin kaura, amma zaman tattaunawar da suka yi da dukkan sassan da abin ya shafe ne ya sa cikin ikon Allah aka samu sauki. Don haka ya yi kira ka jama’a da su kwantar da hankulan su, su cigaba da yin harkokinsu na yau da gobe kamar yadda suka saba domin komai ya riga ya lafa, kana yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo tsarin da zai rage yawan matasa masu zaman banza waɗanda sune maƙasudin tayarda tarzoma da fituttunu a faɗin ƙasar nan. Yace samar da ’yan sandan jihohi abu ne mai kyau da ka iya inganta tsaro a ƙasar nan sai dai yuwuwar hakan zai yi matuƙar wuya in an yi la’akari da yawan kabilu da addinai mabambanta da ke kasar nan.
“Dole ne a yi la’akari da wannan wajen yiwuwar samar da ’yan sandan jihohi, a yi musu horon da za su kawar da bambancin addini ko kabilanci,” inji shi.