Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwarmu cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin.
A yau kuma, inshaAllah, bayani zai gudana kan yadda soyayyar ma’aurata kan sami matsala, har ta zama sarkakkiyar, wacce ma’aurata ba su amfanuwa da ita; da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Dalilan Sarkewar Soyayya: Soyayyar ma’aurata na rikidewa daga kyakkyawa mai dadi mai alafanu, zuwa ga sarkakkiya maras alfanu a bisa bijirowar wadannan dalilan:
• A dalilin matsala a cikin yanayin dangantakarsu da juna, wacce halin zamantakewar yau da gobe ke haifarwa, sannan ya kasance ma’aurata sun jingine wannan matsala gefe guda ba tare da yin wani kokarin warware ta ba.
• A dalilin rashin samun biyan bukatun da suka yi tsammanin samu daga juna; wannan zai haifar da shaukin jin haushin juna a tsakaninsu, wanda ka iya kai su ga tunanin da ma ba su yi auren ba tunda bai haifar masu da abin da suka yi mafarkin samu ba.
• A dalilin wani canji maras dadi da ya fado cikin rayuwar aurensu ko wata musiba da aka jarabci dayasu ko dukansu da ita.
Haka kuma ma’aurata sun kasu gida biyu ta yadda soyayyasu ke zama sarkakkiya:
1. Yawanci, soyayya ta fi sarkewa ga ma’auratan da suka faro aurensu cike da so da kauna da kyawawan shau’uka. Lokacin da zafin soyayyarsu ya yi sanyi, sai su fara ganin wasu abubuwan da ba su yi musu ba, game da juna, wanda da can dumi da zakin soyayya ya boye su ba su ganinsu.
2. Wasu ma’aurata za su fara aurensu da sarkakkiyar soyayya, a dalilin rashin fahimtar juna da rashin yarda da juna, ko ya kasance daya ne yake korafin daya, don haka sai soyayya ta sarke. Ta yiwu, in zama ya yi zama, shakuwa ta haifar da fahimtar juna tsakaninsu, sai sarkuwar soyayyarsu ta warware, ta yiwu kuma su kasa dacewa da cimma wannan, sai soyayyarsu ta yi ta tafiya a sarke, ba su amfanuwa da ita, cikakken amfani.
Sinadaran Sarkakkiyar Soyayya:
1. Banbancin Jinsi: A bayyane yake cewa akwai bambanci mai fadin gaske tsakanin jinsin namiji da na mace. Wannan bambanci ba ga sifffar halittar jikinsu kadai ya takaitu ba, har ma da yanayin halayya, dabi’a, shau’uka da yanayin kaifin hankalinsu. Wannan shi ya haifar da bambancin bukatu da bambanci wajen bukatar da kowannensu ya fi baiwa muhimmanci; abin da mace ta dauka da matukar muhimmanci, a wajen namiji wannan ba abu mai muhimmanci ba ne. Haka kuma abin da namiji ya fi baiwa muhimmanci, wannan abin ba komai ba ne a wajen ’ya mace. Abin da yake burge mace ba shi yake burge namiji ba, haka kuma sha’awar mace ba ita ce ta namiji ba. Namiji hankali ne ke jan dabi’arsa, yayin da mace shau’uka ne ke jan dabi’arta.
Yadda Za a Warware Wannan Matsala: Ma’aurata zas u kawar da wannan matsala ta bambancin jinsi don ganin bai haifar da sarkewar soyayyarsu ba ta hanyar yin amfani da ka’idojin da Allah SWT, Mahallicinsu, mafi sani ga abin da ya fi dace da su ta kowane fanni na rayuwarsu, ya shimfida masu cikin Littafinsa Mai tsarki.
• Ayoyin kur’ani sun nuna namiji shi ne shugaba, jagaba, abin dogaro ga mace a wurare daban-daban ko cikin sigogi masu cike da hikimomi masu alfanu:
1. Ta hanyar ambatar sunan wakilin namiji a kan hukunce-hukunce da bayanan da suka kunshi duka jinsin biyu: namiji da mace;
2. Da kuma, musamman, cikin Aya ta 34 cikin Suratul Nisa’i, inda Allah Madaukakin Sarki Ya fada cewa: “Maza masu tsayuwa ne a kan mata, saboda abin da Allah Ya fifita sashensu da shi a kan sashe, kuma saboda abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu; to salihan mata, masu da’a ne masu tsarewa ga gaibi saboda abin da Allah Ya tsare…”
Don haka, don samun rayuwar aure ta yi kyau, ta yi dadi, sai kowane daga cikin ma’aurata ya taka rawar da ta dace da jinsinsa a bisa ka’idar wannan aya mai albarka ta wadannan hanyoyin:
• Namiji ya tsayu sosai ga matarsa; ta hanyar yin hidima gare ta daga dukkanin abubuwan da Allah Ya fifita shi da su sama da na matarsa:
1. Yi mata hidima da kaifin hankalinsa da ya dara nata; ta hanyar yin amfani da cikakken hankalinsa wajen yin zamantakewa da ita, wannan ya kunshi tarbiyyantar da ita zuwa ga mafi kyawon dabi’u; tsare ta daga fadawa abubuwan da za su zamo mata matsala; yin hakuri da ita, (wajen) kai zuciya nesa da horas da ita a mafi dacewar lokuta; da yi mata wayau, don kwantar mata da hankali, yaye mata wata damuwa ko kawar da wata fitinarta a lokaci mafi dacewa, da sauransu. Zai yi amfani da hangen nesansa da ya fi nata wajen lura da yanayin da take ciki kodayaushe, da lura da yanayin cancanzawar bukatunta, bukatun auratayyarsu don sanin yadda zai huldance ta a kowane lokaci.
2. Dole ya yi mata hidima da karfin mazantakarsa ta hanyar ciyarwa, sutura, muhalli da sauran bukatun yau da kullum; da kuma biya mata bukatun sha’awarta, da kare darajarta da mutuncinta daga batanci.
Ita kuma mace, za ta taka rawa a cikin auratayya ta wadanna hanyoyin:
1. Za ta nuna so, ta zama saliha. Salihanci ya kunshi kyawon dabi’a, kyautata mai hulda da mutane ta kyakkyawar siga, da dagewa wajen tsayar da addininta.
2. Sannan kuma ta kasance mai da’a: Watau ya kasance mace ta kai matuka kwarai wajen yin hakurin biyayya ga mijinta a cikin dukkanin umarni ko haninsa gare ta, matukar ba su saba ma shari’a ba. Yana daga cikin yin da’a mutuntawa, darajtawa da girmama miji a kodayaushe; yana daga cikin yin da’a kokarin faranta masa rai a kodayaushe don guje ma duk wani abin da aka san zai bata masa rai.
3. Sai kuma mace ta zama mai tsare kanta, sirrin mijinta da mutuncinsa a kodayaushe, musamman a lokacin da ba ya tare da ita; kar ta bayyanar da adonta ko soyayyarta ga wasu mazan; kar ta fadi sirrinsa ga wasu kuma kar ta keta mutuncinsa ga wasu. Ta zama mai tsare komai da ya shafi mijinta a kowane irin lokaci.
Don haka har in ma’aurata kowanensu zai taka rawarsa a cikin auratayya, a bisa ka’aidar dokokin zamantakewar da Allah SWT Ya shar’anta a kan kowanensu, to da wuya su samu sarkewar soyayyarsu.
Sai sati na gaba, inshaAllah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.
Yadda Sarkakkiyar Soyayya Ke Faruwa
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwarmu cikin wannan fili, da fatan Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da…