✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ruwan sama ya ci yaro a garin Abekuta

Jama’ar unguwar Sabo Abekuta sun wayi gari da alhinin rashin wani yaro dan kimanin shekaru 15 mai suna Shamsu  da ruwan sama ya tafi da…

Jama’ar unguwar Sabo Abekuta sun wayi gari da alhinin rashin wani yaro dan kimanin shekaru 15 mai suna Shamsu  da ruwan sama ya tafi da shi a makon jiya.

Lamarin ya faru ne bayan da aka yi ta tafka mamakon ruwan sama na tsawon yini guda a ranar Asabar din da ta gabata: ruwan da ya yi sanadiyyar tafiya da yaron, wanda har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a kai ga gano gawarsa ba.

Wakilinmu ya ziyarci kasuwar ’yan gwan-gwan da ke Lafenwa a Abekuta, inda a nan ne ruwan ya tafi da yaron, inda shugaban kasuwar ’yan gwangwan wanda ya shaida faruwar lamarin ya shaida wa Aminiya cewa a daidai lokacin da ake tsaka da tafka ruwan sama ne wanda ya cika ilahirin kasuwar domin ruwan ya cika ta yadda in mutum ya shiga ruwan sai ya kai izuwa kugun sa. 

“Akwai yaran Hausawanmu da ke kawo mana  tallar abinci, sai suka zo daidai babbar kwatar nan suna kokarin shiga da jarka su yi wasa, nan take na hana su, na kore su daga wajen duba da irin hadarin da ke tattare da shiga wajen, amma da yake Allah ya kaddara hakan sai ya faru bayan da na kore su daga nan, sai suka zagaya ta baya, inda suka shiga da jarkoki suna iyo a bisa suna ketare ruwan. To shi yaron tare da yayansa yake ko da yayansa ya ketare shi ma yana dab da ketarewa sai ruwan ya ja shi ya shigar da shi ramin kwatar  da aka gina a karkashin titin jirgin kasa. Bayan da lamarin ya faru an yi kokarin ceto shi, amma lamarin ya faskara sannan an yi ta kokarin nemo gawarsa sai dai har yanzu Allah bai sa an kai ga gano ta ba,” inji shi.

Shugaban ’yan kasuwar ya shaida cewa tunda fari suna kokarin hana yara shiga ruwan domin yin wasa, amma tun da har hakan ta faru za su ƙara daukar mataki don hana sake aukuwar haka a nan gaba.