✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikici ya haddasa mutuwar mutane 12 a Kasuwar Magani

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna ta tabbatar da kama mutum 12 da zarginsu da hannu a rikicin da ya faru a Kasuwar Magani da…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna ta tabbatar da kama mutum 12 da zarginsu da hannu a rikicin da ya faru a Kasuwar Magani da ke karamar Hukumar Kajuru a jihar.

Rikicin wanda ya faru a ranar Litinin da ta gabata ya yi sanadiyyar mutuwar mutum sha biyu, wasu kuma masu yawa sun samu raunuka iri daban-daban, inda wasunsu ke karbar magani a asibiti da ke a Kaduna, kamar kuma yadda ya yi sanadiyyar kona gidaje da shaguna a garin.

Rundunar ta ce mutane sha daya aka kashe a ranar da rikicin ya faru amma mutum daya ya rasu a washegari a wani asibiti a Kaduna.

Kwamishinan ’yan sanda a jihar ta Kaduna, Austin Iwar ne ya tabbatar da kama mutanen tare kuma da yawan wadanda suka rasa rayukansu a garin ga manema labarai. Rahotanni daga garin na nuna cewa rikicin ya samo asali ne a sakamakon sabani da aka samu a tsakanin wasu matasan Kirista da na Musulmi a kan ’yan mata.

Aminiya ta fahimci cewa wasu ’yan mata ne suka nemi canza addininsu saboda soyayya amma sai wasu matasan suka nuna adawarsu da hakan, wanda hakan ya janyo rikicin da ya yi sanadin rasa rayuka tare kuma da lalata dukiya.

Aminiya ta samu ganawa da wasu mazauna yankin ta wayar tarho, inda suka nuna cewa yanzu dai kura ta lafa a sakamakon girke jami’an tsaro da gwamnatin jihar ta yi. Yahaya, wanda aka fi sani da dan Najeriya mazaunin Kasuwar Magani ne kuma ya bayyana wa Aminiya cewa kura ta lafa a bakin kasuwar. Sai dai ya nuna cewa an yi asarar dukiya da kuma rayuka a sakamakon rikicin, inda ya tabbatar da cewa a ranar da rikicin ya faru ya ga gawarwaki uku da idonsa da aka kashe.

Shi ma Baba Ado wani magidanci a yankin, wanda kuma ya kubuta daga hannun maharan da suka sare shi a hannun hagu, ya ce yana tsaye a kofar gidansa ne aka sare shi. “Ina tsaye a kofar gida kawai sai na ji saukar sara a hannuna. Na tambayi wanda ya sare ni abin da na yi masa amma sai kawai suka ruga a guje. Matasa ne suka aikata wannan ta’asa domin har sun halaka wani almajirin  makwabcina. Wannan lamari ya ba mu mamaki matuka,” inji shi. Shi ma ya ce zuwan jami’an tsaro ya taimaka matuka domin sun kora kowa cikin gida.

Gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa ta hannun kakakinta, Samuel Aruwan, inda ta bukaci jami’an tsaro su tabbatar da sun kama duk wani mai hannu a rikicin. A cewar gwamnatin, ba za ta zura ido tana kallon wasu na neman jefa jihar cikin rikicin addini ba.

Kwamishinan ’yan sandan Austin ya ce tuni rundunarsa ta fara binciken musabbabin wannan rikici sannan kuma ya ce wadanda aka kama za a kai su gaban shari’a.

Hukumar ba da agajin gaugawa ta jihar (SEMA), ta bakin shugabanta Ben Kure, ya ce tuni Gwamnan jihar, Nasiru El’rufa’i ya ba su umurnin cewa su tabbatar sun kai tallafi ga wadanda lamarin ya shafa. Don haka sai ya yi kira ga jama’a da su rika kauce wa duk wani abu da zai kawo rikici a tsakaninsu. “Mutane ya kamata su gane cewa rikici babu inda zai kai su, domin yanzu barnar da aka yi a Kasuwar Magani abu ne da ya shafi tattalin arzikin yankin,” inji shi.