✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Najeriya ta ciyo bashin dala biliyan 60 – Ngozi

Aminiya: Wadanne irin nasarori kike ganin kasar nan ta amfana da su a karkashin jagorancinki na ministar kudi? Dokta Ngozi: Da farko ba mu taba…

Aminiya: Wadanne irin nasarori kike ganin kasar nan ta amfana da su a karkashin jagorancinki na ministar kudi?

Dokta Ngozi: Da farko ba mu taba buya ba saboda tsoron girman aikin da ke gabanmu. Aikin gwamnati aike ne da ya hada da bayyana wa jama’a irin aikace-aikacen da kake gabatarwa musamman a kasa irin Najeriya, inda sahihin aikin yake da wuyar fahimta. Mutane suna ganin cewa kan wajen ne domin wata bukatar kanka.
Aminiya: Wane hali tattalin arzikin kasar yake ciki?
Dokta Ngozi: Akarkashin wannan gwamnati mai barin gado mun cimma nasarori ta fuskar tattalin arziki. Ba za a iya sauya tarihi ba domin ba wani gagarumin yunkurin da yake nuni da hakan. Babu wani mutum da zai iya sauya farashin gangar mai da kashi 50 cikin 100, kasar nan ta yi asarar kashi 50 cikin 100 na kudin shigarta. Amma hakan ba laifin shugaban kasa ba ne ko kuma Ngozi Okonjo-Iweala. Wannan ya sa shekarar ta zama mai wahala ba domin wasu sun yi almundahana da tattalin arzikin ba saboda ina da tabbacin cewa ba a samu hakan ba daga bangarena.
Aminiya: Me ya kawo rikici tsakanin gwamnati da kungiyoyin dillalan mai?
Dokta Ngozi: A kowace shekara, dillalan suna aikawa da bayanan adadin man da suka samar ga hukumar kayyade farashin mai wato PPPRA. Daga nan ita zata duba kuma hakan yana faruwa ne a kullum. Wannan ya sa babu wani abu da kammala biyan kudi saboda abu ne da ake ci gaba da yi duk tsawon shekara. Yana da kyau a fahimci cewa duk da wannan mawuyacin halin da muke ciki na rashin kudi hakan bai sanya mu mun fasa biyan kudin tallafi ba.
Tun daga watan Disambar bara mun biya akalla naira biliyan 500. Kada a manta da cewa akwai wasu ’yan kwangila da suma suke so a biya su kudin aikin da suka gabatar. Bayan mun bisu naira biliyan 156, sai dillalan suka ce akwai sauran naira biliyan 200, amma bayan da muka bincika sai muka fahimci cewa naira biliyan 159 ne. Na yi mamaki matuka saboda yadda darajar kudinmu ya fadi hakan bai kamata ya faru ba.
A gaskiya ni a fahimta ta dillalan nan suna so ne kawai su jefa ’yan Najeriya cikin wahala. Kada wani ya yi tunanin cewa matsalar da ta faru saboda suna bin mu bashi ne. Za a jirasu domin a tabbatar da hakan, ko wannan gwamnati ko kuma sabuwar gwamnati da aka rantsar. Bai dace ace ’yan Najeriya suke fadwa wahala ba. Mutane sun san cewa a kasar nan duk wani abu da ya faru, sai ace gwmnati da dillalai su ne da laifi. A lokacin da na kama aiki a watan Agustan shekarar 2011, suna bin gwamnati naira triliyon daya da biliyan 300, amma babu wanda ya rufe ko ina.
Aminiya: Akwai wasu ’yan siyasa da suka ce ana bin wannan gwamnati bashin dala biliyan 60, me ye gaskiyar batun?
Dokta Ngozi: Ni ma na karanta cewa Shugaba Goodluck Jonathan zai bar wa sabuwar gwamnati bashin dala biliyan 60. Bazan yi karin bayani ba kan haka. Amma wannan ba sabon abu ba ne a bayyana bashin da ake bin kasa, kudin da ake bin Najeriya bashi ya kai dala biliyan 53 da biliyan 700. Wannan shi ne jummullar duka bashin da ake bin mu wanda za mu biya cikin shekara 40. Wannan ana magana bashin da kasar nan ta ciyo tun shekarar 1960. Saboda haka wannan bashin ba ya taru ba ne lokacin mulkin Shugaba Jonathan. Kuma ya kunshi bashin da ake bin Gwamnatin Tarayya da sauran jihohi.