✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda na zama mai daukar aiki daga mai neman aiki’

Aminiya: Ta ya ka zamo mai dogaro da kansa harda daukan wasu suna taya ka aiki a shagon sayar da kayan masarufi?  Abubakar Kangiwa: Sunana…

Aminiya: Ta ya ka zamo mai dogaro da kansa harda daukan wasu suna taya ka aiki a shagon sayar da kayan masarufi? 

Abubakar Kangiwa: Sunana Abubakar Umar Kangiwa. Bayan na kamala karatun digiri na farko a 2006 sai na fara neman aiki a 2007. Na rubuta takardu iri-iri har zuwa wurare da dama kamar Babban Bankin Najeriya wato (CBN) da wasu bankuna da manyan kamfanoni da dama. Na je na yi jarrabawan daukan aiki, amma shiru ka ke ji kamar an shuka dusa. Wannan ya sa na zauna na yi tunanin cewa ai tsimi da tanaji na karanta, me ya sa bazan fara kasuwanci ba. Sai na fara saye ina sayarwa. Don kasuwanci sana’ar gidanmu ce. Haka ya sa na rungumeta gadan-gadan. Don a gidanmu ba mai zaman banza, dole ne ka shiga harkan kasuwanci don dogaro da kai. Ya kamata matasa su sani cewa sai an sha wuya akan sha dadi, kamar yadda Dokta Maman Shata ya fadi.  
Aminiya: Ta yaya ka fara? 
Abubakar Kangiwa: A nan Kaduna na tashi, kuma ni mai jama’a ne don ina da haba-haba. Mutane suna kuskuren cewa sai sun yi aikin ofis na albashi wanda kuma baya samuwa kamar da don masu neman sun yi yawa matuka.  
Aminiya: Bayan sayar da kayan masarufi, wadanne irin harkoki kake yi? 
Abubakar Kangiwa: Ina harkan saye da sayar da hannun jari ta hanyar yanar gizo wato intanet (FOREd). Amma yanzu haka ina ci gaba da harkar saye da sayar da gidaje.  
Aminiya: Ko ka taba fuskantar wani kalubale daga abokan hurdaka?
Abubakar Kangiwa: A wannan kanti da na sawa suna Balad wato a harshen Larabce birni ke nan, na sami masu ba da kudi da hannun hagu, da halaye masu kyau da marasa kyau matuka. Amma wanda ba zan manta ba shi ba shi ne wanda wani matashi ya sha kwaya ya yi mankas ya shigo ya dauki waya ta ya juya ya sa aljihu ya fita, sai na sa masu mini aiki su rike shi na ce kar su doke shi, su karban mini wayan kawai. 
Aminiya: Ya kake yi da matsalar wutan lantarki don kana da kaya a na’urar sanyaya kaya maganin kar su lalace? 
Abubakar Kangiwa: Yanzu dai abin ya dan fara inganta, amma matsalar wuta na dagula harkan kasuwanci da sauran mu’amala a kasar nan matuka.
Aminiya: Kamar da jarin nawa mutum zai iya fara irin wannan kasuwanci na babban shagon sayar da kayan masarufi?
Abubakar Kangiwa: Ni dai da kadan na fara, sannan ya dace mutum ya yi nazari ta hanyar tambayan masu irin wannan harkan don ganin ko da riba ko babu, wurin da mutum zai baje koli, lantarki da uwa-uba tsaro da sauransu. Babban abin kula shi ne da sannu ake fara cin riba ba rana daya ba. Don mai hannun jari da yawa da bai iya bi da mutane ba da ma’aikatansa ba zai yi saurin faduwa warwas a kasuwanci da al’amuran duniya. Don ka ga ina da albashi ba wai kawai ina daukan kudi ne muraran in kashe ba. 
Aminiya: Wace shawara za ka ba matasa?
Abubakar Kangiwa: Abu na farko da ya kamata su fahimta shi ne duk wanda aka mai dashi dan-gata to an cuce shi don ranar da mahaifi ko mahaifiya suka rasu ko kudi ya kare, to zai gane cewa bashi da wayo. Neman na kai da kaucewa shan kwayoyi shi ne mafita. 
Aminiya: Shin yanzu idan aka ba ka aikin gwamnati, za ka yi? 
Abubakar Kangiwa: Ai ba wanda zai iya biya na albashi. Domin ba zan iya yin aikin albashi ba. Dalilina shi ne a duk wurin da za a dauke ni aiki za a takura ni, za a iya mayar da ni wani garin da ba zan so in zauna a can ba, da dai sauransu.