✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na fara shirin ‘Lafiya Uwar Jiki’ a Muryar Amurka – Dokta Ladan

Dokta Muhammad Ladan, mai kimanin shekara 60 farfesan bincike kan harhada magunguna ne, kuma shi ne yake amsa tambayoyin jama’a a mashahurin filin nan na…

 Dokta Muhammad LadanDokta Muhammad Ladan, mai kimanin shekara 60 farfesan bincike kan harhada magunguna ne, kuma shi ne yake amsa tambayoyin jama’a a mashahurin filin nan na ‘Lafiya Uwar Jiki’ da Sashin Hausa na gidan rediyon Muryar Amurka ke gabatarwa. Mahaifinsa Alhaji Audu Ladan shi ne akanta na farko a Hukumar Raya Birnin Tarayya, Abuja (FCDA) lokacin da take Suleja. Dokta Ladan da matarsa Annette, suna zaune ne a garin Stone Mountain da ke Jihar Georgia ta kasar USA tare da ’ya’yansu.
A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana yadda ya hadu da Sashin Hausa na Muryar Amurka har ya fara gudanar da shirin Lafiya Uwar Jiki:

Daga Nasir Imam da Salihu Makera

Tarihi:

Na halarci makarantar firamare ta Dawaki da ke Suleja, kafin na zarce Kwalejin Gwamnati ta Keffi, sannan na dan halarci Jami’ar ABU da ke Zariya kafin in tafi Amurka. Na yi digirina na farko a makarantar Clark College, Atlanta (1981) sai na halarci makarantar hada magunguna ta Southern School of Pharmacy, a Jami’ar Mercer Unibersity (1983 da 1987), inda na digiri na daya kan Kemistiri da digiri na daya a Kimiyyar Harhada Magunguna, sai digiri na uku Kimiyyar Harhada Magunguna. Kuma na yi aiki cibiyar maganin cututtukan zuciyya ta Atlanta, Georgia, USA cardiology GRP inda na yi bincike kan cututtukan zuciya da ciwon suga.
 
Shin akwai bambanci tsakanin abin da ka sani a Najeriya a baya da kuma yanzu?
Al’amura suna da sauki a baya, amma yanzu mutane suna shan wahala, a Amurka ma al’amura sun canja.

Me za ka ce kan Suleja da ke Jihar Neja inda ka taso, shin akwai wani canji da ka ga an samu?
Suleja karkara ce a baya da ’yan motoci kadan da babura, amma yanzu akwai cunkoson ababen hawa kuma hanyoyi babu kyau, akwai mutane da dama da suka yiwo kaura lamarin da ya sa jama’a suka karu a garin.

Yaya za ka kwatanta aikin jarida a Amurka da Najeriya, ko akwai wani bambanci?
Ba san abu sosai a kan aikin jarida a Najeriya ba, amma a Amurka suna bin ka’idojin aikin jarida sau da kafa babu rashawa ko makamancinta, kuma babu wanda zai nemi ka karya ka’ida.
 
Kasancewarka likita, yaya ka kalli bangaren kiwon lafiya a Najeriya, shin akwai wani ci gaba?
To, kamar muna komawa baya duk da cewa akwai damar da za mu ci gaba. Kwanaki na ziyarci Babban Asibitin Suleja kuma hankalina ya tashi kan rubabbun kayan aikin da na gani. Idan marar lafiya ya je wannan asibitin akwai yiwuwar cutarsa ta dada muni, wajibi ne gwamnati ta kara ba da kula ga harkokin kiwon lafiya.  

 Yaya aka yi ka fara da Muryar Amurka?
Lamarin ya samo asali ne lokacin da na ziyarci birnin Washington DC shekaru da dama da suka gabata, matata ta halarci wani taron bita, to sai na yanke shawarar in ziyarci gidan rediyon Muryar Amurka, sai wani Ibrahim Biu ya ce akwai mace da take kula da harkokin kiwon lafiya da Hausa, kuma tana shirin barin gidan rediyon, sai ya tambaya ko na san wanda zai iya maye gurbinta. Ni da Jummai Ali sai muka tattauna kan lamarin, to ta haka na fara. Wannan ya faru ne a 1987 zuwa 1988, kuma tun daga lokacin nake gudanar da wannan shirin.

Ko kana yawan ziyartar Najeriya?
Dukkan dangina suna nan Najeriya, ni kadai ne nake zaune a Amurka, a baya nakan ziyarci Najeriya sau daa ne a shekara, amma yanzu nakan zo sau biyu ko sau uku ko fiye.

Ko kana duba yiwuwar kafa harkokin kasuwanci a nan Najeriya?
Eh, ina tunani a kai, sai dai babu kyakkyawan yanayin harkokin kasuwanci a Najeriya, kuma irin yadda jami’an gwamnati suke yin abubuwa ba su karfafa gwiwa.
Shin ka yarda cewa yawan masu sauraron Muryar Amurka na raguwa a ’yan shekarun nan?
To, Muryar Amurka mallakar gwamnati ce, don haka tana da ’yancin yada manufofin Gwamnatin Amurka, wannan shi ne kawai abin da zan iya cewa ke nan a kan wannan batu.   
Wadanne ayyuka kake gudanarwa a Amurka?
Ni ne Shugaban kungiyar Zumunta, wata kungiyar ’yan Arewacin Najeriya mazauna Amurka, kuma ina cikin harkokin al’umma da dama da suka hada da aiki a matsayin alkali a gasar kimiyya ta makarantar Midil ta Kulombiya (Columbia Middle School).
Har wa yau na yi aiki a matsayin jami’in al’adu na wata kungiya mai suna Alliance of Nigerian Organizations ANOG, sai mai ba da shawara ga kungiyar Gamayyar Matasan Najeriya (Nigerian Youth Alliance), kuma wakili a KAbA (School Debelopment Project in Nigeria), kuma wakili a kungiyar Masana Harhada Magunguna ta Amurka (American Pharmaceutical Association), kuma wakili a kungiyar Masana Harhada Magunguna ta kasa ta Amurka (National Pharmaceutical Association), kuma mamba a waa kungiyar kwararru da ake kira Nicore Inbestment Group for Professional Nigerians da ke Amurka.
Kuma ni mamba ne a Kwamitin Dattawa na kungiyar ’Yan Najeriya Mazauna kasashen Waje (Nigerians in Diaspora organization- NIDO), kuma ina taka rawa a ayyukan al’ummar Musulmin Afirka mazauna Amurka. Sai kuma kula da harkokin lafiyar ’yan Afirka mazauna Amurka da sauran harkokin da nake gudanarwa kyauta.
 
Mece ce babbar matsalar da ke fuskantar ’yan Najeriya?
Rashin aikin yi.

Kana da kira ga Gwamnatin Tarayya?
Wajibi ne Gwamnati ta daukaka matsayin asibitoci tare da samar da magungunan rigakafi ta yadda talaka zai amfana.

Wane wasa kake sha’awa?
Ni mai matukar son wasan kwallon kafa ne, kuma dan wasan kwallon Kwando, sannan ina wasan kwallon tebur da golf da hawa dutse da keke da kuma sauraron kade-kaden Jazz.