✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda N300 ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 12

Wata takaddama da ta barke tsakanin wani matukin kwale-kwale da fasinjojinsa a kan N300 a tsakiyar teku ta yi sanadiyyar rasuwar mutum 12 daga cikinsu.…

Wata takaddama da ta barke tsakanin wani matukin kwale-kwale da fasinjojinsa a kan N300 a tsakiyar teku ta yi sanadiyyar rasuwar mutum 12 daga cikinsu.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Legas, Hakeem Odumosu, ya ce  hakan ta faru ne sakamakon gardama da ta kaure tsakanin matukin jirgin, Elebiju Bimbo da fasinjojin bayan da ya bukaci su biya N1,500 a maimakon N1,200 da suka saba biya.

Ya ce, matukin jirgin da ya yi lodin fasinjojin daga gabar Kirikiri kan hanyarsa ta zuwa Badagry ya kashe injin din jirgin ne a tsakiyar ruwa ya yi karin kudin daga N1,200 zuwa N1,500.

Ya ce daga nan rigima ta kaure tsakaninshi da fasinjojin, har jirgin ya nutse sakamakon igiyar ruwar da wani babban jirgin ruwa ya hankado musu a lokacin da ya gitta su.

Kwamishinan ya ce, a lokacin da abun ya faru, fasinjoji 20 ke cikin kwale-kwalen amma mutum takwas kadai suka tsira.