A kowace shekara a goman karshe na azumi Musulmi sukan killace kansu ne a masallacin domin ibadar I’itikafi.
Sai dai an sha samun ce-ceku-ce da rahotanni yadda ake samun bara-gurbi suna aikata abubuwan da suka saba wa Musulunci yayin gudanar da I’itikafin.
Wannan ya sa masallatai da dama suka dakatar da ibadar.
A Jihar Legas an tsara I’itikafin a bana bisa wasu matakai da ka’idoji da masallatan suka tanada.
Akasarin masallatan sun fitar da tsarin sayar da fom kuma ta haka ne suka kayyade yawan mutane da za su hallara, kuma yawan kudin fom din ya danganta ne da tsari da hidimar da masallatan suka shirya wa masu I’itiƙafin.
A garin Agege akasarin masallatan da ake yin I’itikafi a ciki sun sayar da fom dinsu ne a kan Naira 10 zuwa dubu 15.
Sai dai Masallacin Ulafa’u da ke Alfanla a Legas ya sayar da fom dinsa ne a kan Naira 2,000 kuma yana daukar akalla mutum 50 sannan masallacin ne ke yi musu hidimar abincin bude-baki da na sahur.
A Masallacin 1004 da ke Legas an fara sayar da fom ne a kan Naira dubu 10 a goma na farkon azumi zuwa lokacin da watan ya raba tare da tsare-tsare da dokoki da aka gindaya.
Haka a Babban Masallacin Gwamnatin Jihar Legas da ke Alausa a Ikeja, ana gudanar da I’itiƙafin wanda akan samu masu ibada daga makwabtan Jihar Legas suna zuwa I’itikafi a masallacin.
Malam Mustafa Muhammad mazaunin Legas ya bayyana yadda ake gudanar da I’itikafi a sassan jihar da jihohin Kano da Jigawa inda ya taba zama mamba a kwamitocin gudanar da I’itikafin.
Ya ce a duk inda ya gani ana gudanar da I’itikafi bai ga masallaci da tsari kamar Masallacin Gwamnatin Jihar Legas da ke Alausa ba.
Ya ce a wannan masallaci a yanzu ana sayar da fom ne ta Intanet, kuma ana kafe sanarwar sayar da fom din a masallacin kimanin wata biyu kafin watan azumi.
“Mutum zai cike fom din ne a Intanet, inda a nan zai karanta dokoki da ka’idojin da kwamitin I’itikafin ya zayyana.
“Idan ya amince ya cike, zai biya kudin fom Naira dubu 15 zuwa dubu 20, idan lokacin shiga I’itikafin ya yi zai tafi da shaidarsa.
“Za a ba shi katin shaida dauke da hotonsa wanda zai ratayawa a wuya, wannan shaida ita ke tantance masu I’itikafin da sauran masallata,” in ji shi.
Ya ce a Masallacin Alausa an tanadi wuri na musamman da sai masu yin I’itikafin ne ke yin ibada a wajen, an kuma killace masu wajen wankansu daban da makewayi, “Sannan ana ba su wajen kwana da kayan shimfida, kuma ana yi masu girki na musamman,” in ji shi.
Kafin zuwan annobar Kwarona a Masallacin 1004 masu i’itikafi na samu Zakka ta Naira dubu 50 daga Zakkar da Alhaji Aliko Dangote ki fitarwa, sai dai bayan annobar sai aka fito da tsarin raba burodi maimakon kudin.
‘I’tikafi ibada ce mai asali sosai’
Da yake yi wa Aminiya karin bayani game da ibadar, Na’ibin Limamin Babban Masallacin Juma’ar Kofar Fada da ke Kafanchan, Malam Musa Bn Ibrahim ya ce I’itikafi na daga cikin sunnonin Manzon Allah (SAW) a watan Ramadan inda yake tattare shimfidarsa ya tare a masallaci a goman karshe na watan.
“Ibada ce da ke da tushe da asali a addini kuma mai dauke da dokoki da ka’idoji da ake so mai yi ya kiyaye.
“Ba a son yin magana in ba ta lalura ba ballantana ta kai mutum ga sakin layi.
“Ba a karancekarancen wasu littattafai na ilimi in ba Kur’ani da littattafan addu’o’i ma’asurat ba.
“Ba a fita waje in ba don biyan bukata ta kewayawa ba.
“Sannan ba a barin masallacin a tafi wani wuri sai ga wanda ya rasa mai kawo masa abinci kuma babu yadda zai yi, wanda a yanzu hakan ma yayi karanci ainun,” in ji shi.
A Kudancin Kaduna, ana gudanar da I’itikafi a masallatan manyan garuruwa da suka hada da Kagarko da Kafanchan da Gwantu da Kachiya da kuma Kauru.
A garin Kafanchan, hedikwatar Karamar Hukumar Jama’a, manyan masallatan Juma’a biyu ne ake gudanar da I’itikafi kowace shekara a cikinsu, sai dai aikin ginin babban masallacin Jama’atu Izalatil Bidi’ah wa Ikamatis Sunnah na garin Kafanchan da ake kan yi ya sa tsawon lokaci ba a gudanar da I’itikafi a ciki.
Lokacin da Aminiya ta leka Babban Masallacin da ke Kofar Fadar Sarkin Jama’a, ta tarar da masu da I’itikafi, inda wani Malam Muhammad Nasir Is’hak da aka fi sa ni da Malam Abba ya shaida wa wakilinmu cewa daya daga cikin sirrin I’itikafi kamar na zuwa aikin Hajji ne ko Umara ne, ta yadda duk wanda ya taba yi sau daya, ba zai gushe ba wajen ci gaba da zuwa a kowace shekara.
“Duk da ban taba zuwa aikin Hajji ko Umara ba, amma abin da wadanda suka je suke fada shi muke ji duk sa’ilin da shiga I’itikafi ya yi.
“In ba wata lalura ba duk wanda ya saba shiga I’itikafi ba ya fata ya daina shiga saboda tana dauke da sirruka da dama,” in ji shi.
Hamisu Hamisu mai shekara 15 da Muhammad Ya’u yaro mai shekara 12 sun ce a daidai lokacin da takwarorinsu ke waje suna dokin zuwan ranar Sallah sun gwammace shiga masallaci domin aiwatar da ibada don neman taimakon Allah a rayuwarsu da kuma nema wa iyayensu da sauran al’ummar Musulmi gafarar Allah.
Ya’u ya ce ya fara I’itikafi ne tun yana da shekara 10, shi kuma Hamisu ya ce bai san lokacin da aka fara zuwa da shi ba, amma dukkansu sun ce a sanadiyyar yayyensu da suke kai musu abincin budabaki daga gida ne suka fara sha’awar shiga I’itikafin.
Shu’aibu Mahammad Sani, ya kwashe shekara goma yana I’itikafi a Masallacin Sheikh Dahiru Usman Bauchi da ke garin Kaduna.
Ya shaida wa wakilinmu cewa kulla zamunci da bautar Allah cikin natsuwa da kwanciyar hankali na daga abin da ya fi burge shi a ayyukan I’itikafi.
Malam Ahmad Usman, daya daga cikin wadanda suka assasa I’itikafi a Masallacin Juma’a na Kafanchan, ya shaida wa Aminiya cewa lokacin da suka fara I’itikafi a masallacin jama’a na ta mamaki a kai, amma zuwa yanzu ya zama ruwan dare kowa na sha’awa.
“An wuce marhaloli da yawa har zuwa halin da ake ciki inda za ka ga yara matasa na shaukin shiga da kuma kokarin yin ibadar I’itikafi,” in ji shi.
Sai dai ya bayar da shawara a rika shirya bita ta musamman na wasu kwanaki kafin da kuma cikin Ramadan don horar da masu sha’awa musamman matasa da kananan yara game da ka’idoji da dokokin I’itikafin da sirrika da alfanu da falalarta don kiyaye duk abin da ka iya bata musu I’itikafin.
Shugaban Kwamitin I’ltikafi na Babban Masallacin Juma’ar, Armaya’u Nababa ya ce a bara akalla mutum 160 ne suka shiga ibadar.
An dawo I’itikafi a Masallacin BUK bayan shekara uku
Aminiya ta leka Masallacin Juma’a na Jami’ar Bayero, wanda aka yi sama da shekara 30 ana I’itikafi a cikinsa.
Malam Murtala Garba shi ne Ladanin Masallacin ya ce rabon da a gudanar da I’itikafi a masallacin tun shekarar 2019 saboda bullar Kwarona.
Malam Murtala ya ce tun azumi na kwana 15 suka fara rarraba fom ga masu bukatar yin wannan ibada inda suka tantance tare da fara wannan ibada a ranar 20 ga Ramadan.
Ya ce suna da dokokin da suka hada, “Ba a cin abinci a cikin masallaci. Kuma ba a yin hira ko waya marar amfani. Alhamdulilahi a wannan karo ma ban ga wanda ya zo da waya ba,” in ji shi.
Malam Murtala ya ce kasancewar mutane daga wajen jami’a da cikinta suna zuwa Tahajjud, sun dauki matakin tantancewa bayan an yi idar da Sallah don tabbatar wa wadanda ba su cikin masu I’itikafin sun bar masallacin.
Amira Halima Zakariyya ita ce shugabar bangaren mata masu I’itikafi, ta ce, “Gaskiya ba mu da wata matsala da mu kanmu masu yin I’itikafin, kowace tana iya kokarinta wajen ganin ta yi abin da ya dace.
“Idan gari ya waye mukan hada kanmu mu share cikin masallacin mu kuma wanke ban-dakuna.
“Babbar matsalar da muke fuskanta ita ce ta dalibai mata da suke shigowa da rana domin yin Sallah.
“Wasu za ki ga ba Sallah suke zuwa yi ba, sai dai su zauna su yi ta hira suna yin waya suna damunmu da surutu.
“Ko kuma ki ga sun zo sun yayyaga takardu sun tafi sun bar su haka.”