✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muke mayar da tsofaffin roba dukiya –‘Yan bola jari

Unguwar  Gwazunu da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a yankin karamar Hukumar Suleja ta Jihar Neja ta shahara a wajen ayyukan sarrafa sharar roba…

Unguwar  Gwazunu da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a yankin karamar Hukumar Suleja ta Jihar Neja ta shahara a wajen ayyukan sarrafa sharar roba zuwa dukiya inda matasa ke yin abubuwa iri-iri daga robar da suka narka kamar kofi da buta da jakar leda da sauran abubuwa masu amfani. 

Aikin wanda suke gudanar da shi ta hanyar amfani da wasu manyan injuna irin na masana’antu, na gudana ne dare da rana don cika alkawuran da su ka dauka a tsakaninsu da masu bukatan kayayyakin wadanda ke safararsu zuwa wasu garuruwan Najeriya da ma ketare, kamar Nijar da Kamaru da Chadi da Mali da kuma kasar Afirka ta tsakiya, kamar yadda su ka bayyanawa Aminiya. 

Malam Ibrahim Umar, daya daga cikin masu injunan sarrafa sinadarin roba zuwa wani abun amfani, ya ce da inji daya yake kera kofi da roban cin abinci da kuma butar alwala. Ya ce yana amfani da mabanbantan fayafayai a duk lokacin da yake son yin daya daga cikin abububuwan don koda roba zuwa abin da a ke son a yi. “A yanzu haka an bani sautun yin kofuna da a kullum nake yin kamar dubu 1 a yini sannan wani dubu 1 da dare inda ma’aikatana ke aikin karba-karba don ganin mun kammala aikin kafin lokacin da muka yi alkawari.”

Sai dai masu aikin sun yi korafi a kan makudan kudi da su ka ce kamfanin wutar lantarki na dora masu tun bayan fara amfani da tsarin mita, inda a dalilin hakan injinsu ke neman zama mara riba bayan sun biya makudan kudin wuta. 

Wani mai masana’anta a wajen mai suna malam Nura Muhammad da ya mallaki nau’ukan injuna daban-daban na aikin ya ce a baya yana da ma’aikata kamar 150, sai dai a sakamakon karin kudin wuta da kamfanin wutar lantarki ke karba daga hanunsu a yanzu bayan kaddamar da tsarin amfani da mita, dole ta sa ya rage adadin ma’aikatansa zuwa 70.

Malam Nura wanda ya ce ya na cikin sana’ar sama da shekara 30 ke nan yanzu ya kara da cewa ma’aikatan nasa sun hada da masu nika roba da masu wankewa don rabata da tsakuwa ko datti kafin a shanyata, da da sauransu, ya ce a yanzu ya fi maida hankali ne a bangaren yin jakar leda kadai bayan fuskantar matsalar. Haka nan ya ce sinadarin da suke sawa robar bayan narkar da ita don ba ta launin da a ke bukata, sun yi tsada tun bayan tashin farashin dala, kasancewar ana kawota ne daga kasar waje.

Wani jagora a bangaren nemo roba da kuma sarar da ita ga masu sarrafata, malam Abubakar Baba Abdullahi, ya ce baya ga sayan robar da yake yi daga hannun ’yan bola jari, yana kuma da ma’aikata da ke karkashinsa da ke zuwa wuraren tara shara daban-daban da ke yankin Birnin Tarayya Abuja suna tsinto masa sharar roba, inda a wata guda yake tara kamar tan 400. Ya ce farashin kilon roban ya kama daga naira 40 zuwa 50 duk kilo, sai dai a cewarsa a wani zubin ya na kai har naira 100 idan a ka shiga tsananin bukatarsa.

Sannan ya yi kira ga hukumomin gwamnati irin hukumar bunkasa kanana da matsakaitan masana’antu wato SMEDAN da ta kai masu dauki ta hanyar tallafa masu da horo da kuma kayan aiki, sannan ya bukaci da ta sa baki a kan matsalar tsadar wutar lantarki da suke fama da ita a halin yanzu.

Ya ce harkan jari bola na taimakawa wajen samar da dumbin ayyukan yi ga matasa, baya ga rage shara a cikin garuwa , “A saboda haka mu na kira ga hukumar da ta sa mana hannu a lamarin ta yadda idan ya inganta ba sai an shigo da wasu abubuwan roba ba daga kasar waje, inj shi. Masu sana’ar sun ce su na samun sauki wajen tara sharar robar kasancewar yankin nasu na da kusanci da yankin birnin tarayya Abuja, ga kuma rashin manyan masana’antu a wajen da ke irin aikin inda a cewarsu hakan ya sa kayan da su ke yin ke da sauki idan a ka kamanta da na wasu wurare.