✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda muke ba da horo da karfafa sana’a – kungiyar Matasa

Wata kungiyar matasan Arewa da ke Abuja mai suna “Youths Initiatibe for Dibersity in Nigeria” ta nuna damuwa a kan matsalar zaman kashe wando da…

Wata kungiyar matasan Arewa da ke Abuja mai suna “Youths Initiatibe for Dibersity in Nigeria” ta nuna damuwa a kan matsalar zaman kashe wando da matasan Arewa ke fuskanta inda ta bukaci shugabannin yankin su hanzarta shawo kan lamarin ta hanyar hada kai da kungiyoyi ire-irenta da kuma karfafa wa masu kafa masana’antu gwiwa. 

Shugaban kungiyar Malam Nasiru Doka Shinkafi ne ya bayyana haka a yayin zantawa da wakilinmu bayan gudanar da taron kungiyar a ofishinsu da ke garin Lugbe, Abuja.

Ya ce mambobin kungiyar suna sanya wa kansu haraji a duk wata domin tafiyar da ayyukansu sannan suna hada wadanda ke da sana’a a cikinsu da marasa aikin yi kamar daya zuwa biyu inda ake koya musu sana’a, kuma bayan sun koya sai a tallafa masu da jari ko kayan aiki da za su fara tasu sana’a ta kansu. kungiyar ta ce matsalar rashin aikin yi ya fi muni a Arewa idan aka kwatanta da Kudu ga kuma yawan marasa zuwa makaranta da matsalar kai hare-hare musamman a kauyuka inda nan ne  aka fi yin noma ko kiwo kamar Jihar Zamfara.

Shugaban kungiyar ya kara da cewa matsalar shan kayan maye da kuma ayyukan daba ba za ta ragu ba, idan ba an yi yaki da rashin aikin yi ba. “Saboda zuciyar marasa aikin yi tamkar ma’aikatar Shaidan ce, ba za ta saka masa komai ba in ban da sha’awar aikata munanan ayyuka,” inji shi. 

Malam Nasiru Doka ya ce kungiyar tana shirin shirya gudanar da gangami na kasa don gayyatar jagororin al’umma daga yankin Arewa don bayyana masu tsare-tsarensu da kuma neman yadda kungiyoyi irin nasu za su samu hadin kan hukuma domin saukake aikace-aikacensu da kuma kara fadada su.